NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
Published: 14th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.
Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama da waɗanda suka yi karatu mai zurfi.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba matsalar rashin aikin yi da kuma hanyoyin da za a iya bi don magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: karatu Rashin Aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci.
Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar.
Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu“Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi.
Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale a fannin tattalin arziƙi tun farkon mulkinsa, amma ya jaddada cewa matakan da aka ɗauka suna da muhimmanci.
“Muna cikin mawuyacin hali lokacin da na karɓi mulki. Idan ba mu ɗauki matakan da suka dace ba, tattalin arziƙin Najeriya zai durƙushe,” in ji Tinubu.
Ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa abubuwa na ƙara gyaruwa, “A yau, muna kan turbar da ta dace. Farashin canjin kuɗi yana daidaituwa, farashin abinci yana raguwa, musamman a lokacin azumin Ramadan. Akwai nasara a tafiyar.”
Sanata Emmanuel Chiedoziem Nwaka, wanda ya jagoranci tawagar, ya yaba wa matakan Tinubu, musamman shirin bai wa ɗalibai rance domin tallafa wa iliminsu.