Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar  gwamnatin  kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Syria (SOHR) ta sanar da kashe fararen hula 1,383, galibi ‘yan Alawite a cikin makon da suka gabata.

SOHR ta ce yawancin wadanda aka kashe fararen hula ne, kuma jami’an da ke da alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne suka kashe su.

Kasar Rasha ta yi gargadi kan karuwar ta’addanci a kasar Syria tare da kwatanta kashe-kashen da kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda da abin da yake faruwa a yanzu a kasar Syria. Ta yadda masu rike da madafun iko da ‘yan bindigar da ke karkashinsu suke tara daruruwan fararen hula daga bangaren  marasa rinjaye su kashe su baki daya, kamar yadda ‘yan kabilar Hutu suka rika yi wa ‘yan kabilar Tutsi a Rwanda a shekara ta 1994.

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia, ya ce abin takaici  shi ne babu wata kasa a duniya da ta dauki wani mataki domin ganin dakatar da wannan kisan kiyashi da ake yi a Syria.

Hotunan bidiyo da dama sun nuna Kungiyoyin da ke dauke da makamai karkashin inuwar kungiyar Tahrir Sham mai alaka da alkaida wadda kuma itace ta kfa gwamnatia  halin yanzu a Syria tare da taimakon Turkiya da Qatar, su ne suke aiwatar da wannan kisan kiyashi a kan ‘yan alawiyya, bisa hujjar cewa suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Bashar Assad.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha  na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran

Ministan harklokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce kasarsa na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar farko ta Iran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

Mista Lavrov ya jaddada goyon bayan Moscow ga sake farfado da muhimmiyar yarjejeniya da Iran da manyan kasashen duniya suka rattabawa hannu a shekarar 2015.

“Mun tattauna halin da ake ciki a yankin Tekun Fasha da kuma shirin hadin gwiwa,” in ji Lavrov a wata hira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Tass, yayin da yake amsa tambaya kan ko batun Iran na cikin tattaunawar da ake yi tsakanin Rasha da Amurka.

Rasha ta tattauna halin da ake ciki dangane da yarjejeniyar da Iran ta kulla da Amurka yayin da ta ci gaba da tattaunawa kan batun da kasashen Turai, yana mai jaddada maido da yarjejeniyar da ake yi a halin yanzu “wanda Amurkawa suka balle a lokacin gwamnatin Trump ta farko.” »

Lavrov ya bayyana cewa “Rasha za ta goyi bayan ci gaba da tsarin da ya samar da ainihin yarjejeniyar da kwamitin sulhu da Iran suka amince da ita. »

“Za mu ga yadda lamarin zai kasance,” in ji shi, yayin da yake magana kan shawarwarin da ya yi da jami’an Amurka da na Turai.

Ministan harkokin wajen na Rasha ya kuma yi magana kan rahotannin kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya da ke nuni da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a kulla sabuwar yarjejeniyar nukiliya a wata wasika da ya aike zuwa Tehran.

“Amurka na son sabuwar yarjejeniyar nukiliya da Iran don tilasta mata kada ta goyi bayan kungiyoyin da ke gabas ta tsakiya, amma wannan zabin ba zai yi tasiri ba. “Abin damuwa ne yadda Amurkawa su sanya sharuddan siyasa ga wannan sabuwar yarjejeniya,” in ji shi.

Lavrov ya kuma yi watsi da duk wani matsin lamba ga Iran kan tasirin da take da shi a yammacin Asiya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘An Kwashe Shekaru Ana Kashe Kudaden Yaran da ba a ma Haife su ba a Nijeriya’
  • Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Karfafa Huldar Dake Tsakaninta Da Kano
  • Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
  • Shugaba Vladimr Putin Na Kasar Rasha Ya Amince Da Tsagaita Wuta A Yakin Ukraine
  • Masu Goyon Bayan Falasdinu Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Don Bukatar Sakin Mahmoud Khalil A Tsakiyar Birnin New York
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar
  • Rasha  na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran
  • Sharhin Dangane da: Atisayen Damarar Tsaro Ta 2025 Tsakanin Kasashen China, Rasha Da Iran
  • “Yan Ta’addan Syria Suna Boye Gawawwakin Mutanen Da Su Ka Yi Wa Kisan Gilla