Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta
Published: 14th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar.
Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako da ke neman Iran da ta shiga tattaunawa kai tsaye tare da Amurka dangane da batun shirinta na nukiliya.
A baya dai Trump da kansa ya yi ikirari a wata hira da Fox Business cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Jami’ai daban-daban na Iran ciki har da Araghchi, sun yi watsi da ikirarin na Trump.
Baya ga haka kuma Iran ta sha nanata cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa da amurka a karkashin matsin lamba ko barazana ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a tsakanin bangarorin biyu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu sake haduwa, sannan har zuwa karshen tattaunawar. Bayan kammala tattaunawar dai, shugaban tawagar JKI a tattaunawar kuma ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana a shafinsa na X kan cewa, tattaunawar ta yi armashi.