Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu
Published: 14th, March 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci.
Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar.
“Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi.
Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale a fannin tattalin arziƙi tun farkon mulkinsa, amma ya jaddada cewa matakan da aka ɗauka suna da muhimmanci.
“Muna cikin mawuyacin hali lokacin da na karɓi mulki. Idan ba mu ɗauki matakan da suka dace ba, tattalin arziƙin Najeriya zai durƙushe,” in ji Tinubu.
Ya kuma tabbatar wa ’yan Najeriya cewa abubuwa na ƙara gyaruwa, “A yau, muna kan turbar da ta dace. Farashin canjin kuɗi yana daidaituwa, farashin abinci yana raguwa, musamman a lokacin azumin Ramadan. Akwai nasara a tafiyar.”
Sanata Emmanuel Chiedoziem Nwaka, wanda ya jagoranci tawagar, ya yaba wa matakan Tinubu, musamman shirin bai wa ɗalibai rance domin tallafa wa iliminsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya Tattalin Arziki
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta daƙile wani harin ’yan bindiga tare da ceto mutum 30 da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Faskari.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani da ke yankin.
Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Idan Fubara ya yi laifi za a iya tsige shi – Wike“Da misalin ƙarfe 1 na dare, muka samu rahoto cewa wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Unguwar Sarkin Fulani inda suka sace mutum 30,” in ji sanarwar.
Bayan samun rahoton, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka yi wa maharan kwanton ɓauna, sannan suka yi musayar wuta da su.
DSP Sadiq, ya ce babu wanda ya ji rauni daga cikin waɗanda aka kuɓutar, kuma jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da wasu dabbobin da maharan suka sace.