Ranar Mata Ta Duniya: Kalubalen Da Mata Ke Fuskanta A Siyasar Nijeriya
Published: 14th, March 2025 GMT
A Nijeriya sha’anin siyasar mata wani babi ne mai zaman kan sa da mata ke kuka da kokawa kan yadda ake nuna masu kyama da kabilanci a dukkanin jam’iyyu tamkar wani jinsi ne ba na mutane ba.
A bayyane yake cewar gagarumar gudunmuwar da mata ke bayarwa a farfajiyar siyasar Nijeriya ta fi gaban a nanata a bisa ga tasiri da kuri’un su ke yi a kowane irin zabe, sai dai anya suna samun adalci?
Yawan adadin da jinsin mata ke da shi da ya zarta na maza ya ba su cikakkiyar damar tabbatar da nasara ko akasin ta ga ‘yan takarar dukkanin mukamai kama daga kansila zuwa shugaban kasa wanda hakan karara ya nuna karfin ikon da mata ke da shi wajen azata ta zauna a siyasar kasar nan.
Mata da yawa sun zama kallabi tsakanin rawuna ta yadda suke zaburar da mutane da dama kan yadda suke sauke nauyin jagorancin da ke kan su da hannu biyu.
Sai dai duk da kima, tasiri da muhimmancin kuri’un mata a zabukan siyasar Nijeriya suna fuskantar dimbin kalubale a dukkanin al’amurran siyasa tamkar ba su da wata muhimmiyar rawar takawa.
Kama daga kan rashin samun goyon baya daga jam’iyyun siyasa, karancin iyayen gida akasin daya jinsin da siyasar ubangida ta mamaye da juya masu baya a kakar zabe da sauransu manyan kalubale ne da mata ke fuskanta.
Matsalolin cin zarafi, camfe- camfen al”ada da batun addini suna matsayin manya- manyan tarin matsalolin da mata suke fuskanta a siyasar jiya kuma suke fuskanta a siyasar yau wadda idan ba wani sauyi aka samu ba haka lamarin zai ci-gaba da kasancewar a siyasar yau da gobe.
Duk da gagarumar muhimmiyar rawar da mata ke takawa a siyasance har yau akwai karancin gurbin da ya kamata mata su cike a mabambantan wakilci a kujeru daban daban.
Masu fashin bakin lamurran siyasa na da ra’ayin idan da mata na samun cikakken goyon bayan tsayar da su takara kuma babu tasirin addini da al’ada da dimbin nasarar da za su samu a zabe ba karama ba ce musamman bisa ga sadaukarwa da jajircewar da suke da ita.
A gwamnatance da kuma a siyasance, a kowane irin aiki a bayyane yadda aka shaidi jajirtacewa, sadaukar da kai da aiki tukuru da mata suke da shi wajen sauke muhimmin nauyin al’umma da ke kan su wanda a lokuta dama yabo da jinjinar da suke samu wajen aiwatar da gaskiya da adalci ta nunka ta takwarorinsu maza.
Juriyar tsayuwar awa da awanni a cikin rana domin jefa kuri’a, kin goyon bayan hada kai da su wajen murdiyar zabe da sadaukar da kuri’un su ga zaben ‘yan takarar da suke ganin sune maslaha kuma mafita ga al’umma abubuwa ne da mata suka ciri tuta a kai.
Duk da haka yau a siyasance mata na dauke da takaici da haushin yadda aka mayar da su saniyar ware ba tare da godiya, yabawa da sakawa halasci da amanar da suke da ita ta tsayawa kan daka wajen tabbatar da nasarar daya jinsin a kowane irin zabe.
A wurare da dama mata na fuskantar kalubalen tasirin addini da al’ada wajen hana tsayar da su takara ta yadda suke fuskantar karancin goyon baya daga jama’a da kuma jam’iyyun siyasa.
Alkaluman bayanai sun nuna a zaben 2023 da ya gabata kaso 9 ne cikin 100 suka kasance mata wanda a kowane zabe adadin raguwa yake yi tun daga zaben 2011.
A zaben 2023, an samu ‘yan takara maza 13, 725 yayin da aka samu mata 1, 544 kacal kama daga kan takarar shugaban kasa, gwamna, ‘yan majalisar dokoki na jiha da ‘yan majalisar wakilai da na dattawa.
Haka ma mafi yawan matan da ke tsayawa takara suna tsayawa ne a karkashin inuwar kananan jam’iyyu wadanda ba su da tasirin lashe zabe a Nijeriya wadda matsala ce mai zaman kan ta rashin damar da ba su samu a manyan jam’iyyu.
Nijeriya wadda ke da jihohi 36, babu jiha daya a yau da mace ke rike da kujerar shugabanci a matsayin gwamna. Haka ma a Majalisar Dattawa ta 10 wadda ke da masu shata dokoki 109, uku ne kawai mata. Dukkanin matan da suka zauna a majalisa ta tara sun fadi zaben da ya gabata.
A majalisar wakilai kuwa wadda ke da ‘yan majalisa 360, 13 ne kawai mata wanda cikin ma an samu kari ne a kan adadin mata da suka wakilci al’umma a majalisar wakilai ta tara.
Mace mai kamar maza, Dame Birginia Ngozi Etiaba ita kadai ce mace daya tilo da ta samu nasarar zama gwamna a Nijeriya a inda ta kasance mace mafi daraja ta daya a Jihar Anambra a 2006 bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige gwamna Peter Obi, a matsayin ta na mataimakiyar gwamna sai ta gaje shi.
A tsayin shekaru mata da dama a siyasar Nijeriya sun rika kuka da zargin cin zarafi daga takwarorinsu daga shugabannin da ke jagorantar gwamnatoci da hukumomi.
A baya bayan nan a shekarar 2020 tsohuwar shugabar rikon kwarya a hukumar raya yankin Neja- Delta (NDDC) Joy Nunieh ta zargi ministan harkokin yankin, Godswill Akpabio da cin zarafin ta lamarin da ya tayar da kura a wancan lokacin.
Haka ma a 2016 Jakadan Kasar Amurka a Nijeriya James Entwistle ya zargi wasu ‘yan majalisar wakilai uku a Nijeriya da cin zarafin wata baiwar Allah ta hanyar yunkurin yi mata fyade.
A kwanan nan kuma zargin cin zarafin da Sanata Natasha Akpoti- Uduagan da ke wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa ta yi wa shugabar majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya tayar da hazo da haifar da cece- kuce a farfajiyar siyasar ciki da wajen kasar nan.
Hayaggar Natasha da Akpabio ya bude sabon babin kurji da damuwar da mata da yawa suke da na zargin cin zarafi daga shugabanni, haka ma hakan ya kara zama hujjar da magabata, shugabannin addini da mazajen mata ke kafewa a kai na kin baiwa mata damar shiga a dama da su a harkokin siyasa.
Watsi da korafin da Sanata Natasha ta gabatar a majalisa domin binciken zargin badakalar da juya mata baya da mafi yawan takwarorinta ‘yan majalisar suka yi da dakatar da ita na tsayin watanni shida abubuwa ne da al’umma ke kafewa a kan gwagwarmayar harkokin siyasa ba na mata ba ne duk kuwa da amana da nasarar da suke samu ta zarta ta takwarorinsu maza.
Ba shakka idan aka yi la’akari da gagarumar muhimmiyar rawar da mata ke takawa a siyasar Nijeriya, kai tsaye za a iya cewa sun cancanci samun damar rike akalar rike kowane irin shugabanci wanda ko za a samu sauyin karin adadin mata a madafun iko a 2027 da raguwar cin carafinsu da suke zargi? Lokaci zai yi alkalanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Fyade majalisar wakilai siyasar Nijeriya yan majalisar A majalisar a majalisar kowane irin
এছাড়াও পড়ুন:
Matashin da ke kera jiragen sama da bindigogi daga robobi
Malam Yunusa Alfazazi, dan kimanin shekara 35 kuma mazaunin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, ya kafa tarihi a duniyar fasaha da kirkire-kirkire, inda yake kera jiragen sama da bindigogi da sauran na’urori daga robobi da filastik.
Allah Ya albarkaci Nijeriya da mutane masu fasaha da baiwar kera kayayyaki ba tare da samun horo na musamman ba.
Misali, Malam Yahaya Makera da ya kafa tashar rediyo mai aiki a Kaduna da kayan aikin daba su taka kara sun karya ba.
’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?Haka nan, Mansur Nuhu Bamalli ya samu nasarori a fannin injiniyanci duk da karancin kayan aiki da suke fama da shi da kuma rashin goyon baya na musamman.
Malam Yunusa Alfazazi na daga cikin irin wadannan matasan masu hazaka, wadanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen c-gaban fasaha da kirkirekirkire a Nijeriya idan suka samu goyon baya da tallafin da ya dace.
Duk da irin basirarsa, Yunusa Alfazazi ba injiniya ba ne kuma bai taba halartar wata makarantar koyon fasaha ba.
Kai! Bai ma taba halartar wata makarantar zamani ba. Da kansa ya koyar da kansa, ya kuma ci gaba da inganta fasahar tasa a tsawon shekaru ta hanyar gwaje-gwaje da bincike.
Duk da wannan basirar tasa, matasyin yana sana’ar tura baro ne da yin dako wajen samun na rufin asiri, duk da kasancewarsa bai taba aure ba.
Gwamna da Babban Hafsan Tsaro sun yaba masa
Ayyukan Yunusa ba na wasa ba ne, domin yana kera samfurori masu cike da tsari da fasaha, wadanda suka ja hankalin manyan mutane, ciki har da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
A wata ziyara da El-Rufai ya kai garin Kafanchan, ya yi mamakin fasahar Yunusa.
“Gwamna El-Rufai ya tambaye ni ko ni ne na kera jirgin saman da ya gani. Na amsa masa da eh, sai ya ba ni katin tuntubarsa domin mu yi magana kuma na ba shi kyautar helikwaftar.
“ Amma gaskiya ban kira shi ba. Wannan abin ya faru ne lokacin yana gwamna,” in ji Yunusa.
Haka nan, Janar Christopher Gwabin Musa ya yaba da fasahar matashin, tare da sayen daya daga cikin bindigogin roba da ya kera.
“Ya yaba min, ya ba ni kyauta, kuma ya karbi bindigar,” in ji Yunusa, wanda ya ce “ban samu horo na musamman a kan aikin ba.”
Ya dai dogara ne da kokarinsa da baiwarsa kawai tare da lura da yanayin abuguwan.
Ya ce, “Na fara ne da kera kananan motocin roba da bindigogi. Daga baya kuma sai na fara kera jiragen sama.”
Hazakarsa tasa ta kunsshi sarrafa abubuwa daga kayayyakin da aka yi watsi da su zuwa abubuwa masu ban mamaki ne.
Yana amfani da robar danko da filastik don kera samfurorin jiragen sama da bindigogi kala-kala da suka yi kama da na gaskiya.
Abin da ya fi burge mutane game da shi shi ne yadda ba ya amfani da na’urorin aiki na zamani.
Da kayan aiki na yau da kullum da kuma kwarewarsa yake kera kayayyaki masu tsari kamar na gaske.
Jiragensa na sama, ko da yake kanana ne, suna da bangarori masu motsi da ke yin aiki kamar na gaske.
Bindigoginsa kuwa da ya kera daga robobi da filastik, suna daukar hankali, kai ka ce bindigogi ne na gaskiya.
Zan iya fiye da wadannan —Alfzazi
Sai dai duk da kwarewarsa, Yunusa bai samu wata dama da za ta amfane shi ba har zuwa yanzu.
Wannan shi ne irin yanayin da wasu matasan Nijeriya ke fuskanta ta shi na rashin jagoranci ko tallafi daga gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu, lamarin da ya haifar wa da tafiyar Yunusa cikas da kalubale.
Babban burinsa shi ne gwamnati ta dauke shi aiki a wata hukuma da ke kula da kera kayayyaki irin wadannan domin ya ba da tasa gudunmawarsa ga ci-gaban kasa.
Ya ce, “Ina jin zan iya yin fiye da abin da nake yi idan aka ba ni dama. Ina so in zama wani bangare na wani gagarumin aiki domin in taimaka wajen kera kayayyakin da za su amfanar da Nijeriya.”
Rashin tallafi
Amma saboda rashin goyon baya, yana dogaro ne da dan abin da da yake samu daga mutanen da ke sha’awar ayyukansa.
Wani lokaci kuma yana tura baro ne don yin dako domin ya samu abin da zai ci.
“Ba ni da iyali, kuma ba ni da aiki. Nakan samu wasu ’yan kudi ne daga mutanen da ke sha’awar aikina.
“Wasu lokutan kuma sai na yi dako ta hanyar tura baro nake samun abin dogaro a rayuwata. Wannan ne yake ci gaba da karfafa min gwiwa.”
‘Jami’in tsaro ya sa ni a tsaka-maiwuya’
Duk da girmamawar da yake samu, yana kuma fuskantar gargadi daga jami’an tsaro.
Ya ce, “Wani jami’in tsaro ya taba gargadina cewa in kula da kyau kada in rika yada sirrin fasahata ga mutanen da ba su dace ba.
Ya ce in kiyaye sosai kada in sayar da fasahata ga kowa.”
Matashin ya ce, wannan gargadin ya kara jefa shi cikin damuwa da rashin tabbas game da inda zai dosa yanzu da irin wannan fasahar kuma da suwa zai yi hulda har ta kai shi ga samun hadin gwiwa da mutanen da za su iya taimaka masa.
Duk da cewa yana fahimtar tasirin sirri da tsaro da ke tattare da aikinsa, amma yana gudun kada ganin baiwarsa ta tafi a banza.
“Idan da zan samu damar yin aiki tare da hukumomin gwamnati ko masana’antu masu zaman kansu, zan iya amfani da baiwata ta hanyoyin da za su amfanar da kasa,” in ji shi.
Yadda za a ci moriyar basirar
Nijeriya tana fama da matsalar yawan kaurar masu basira zuwa kasashen waje, ko kuma rashin amfani da baiwar da ake da ita saboda rashin damarmaki.
Lamarin Yunusa misali ne na irin mutane masu hazaka da ke fuskantar kalubale a kasar da ke neman ci-gaban fasaha.
A yayin da ake kokarin kera kayayyakin soja da na tsaro a Nijeriya, ana bukatar matasan irin Yunusa su samu goyon baya, a maimakon barinsu da ake yi su kasance ba su ga tsuntsu ba su ga tarko.
Ya kamata gwamnati da kungiyoyi su fara karkatar da hankalinsu ga irin wadannan mutanen masu basira.
Idan aka ba shi horo da jagoranci, Yunusa zai iya zama kwararre a bangaren fasaha da kirkire-kirkire.
Idan aka ba shi tallafin ilimi, zai iya zurfafa bincike da kirkirar sabbin abubuwa. Idan kuma kamfanoni masu zaman kansu suka tallafa masa, zai samu damar fadada ayyukansa.
Yadda za abunkasa basirarsa
“Baya ga tallafin kudi, abin da Malam Yunusa ke bukata shi ne haduwa da kwararru a fannin injiniyanci da za su jagorance shi kan hanyoyin da suka dace.
Ta hakan, zai iya fahimtar fasaha yadda ya kamata kuma ya kera kayayyakin da za a iya fitarwa kasuwanni.
“In har aka kula da shi yadda ya kamata, na iya zama wani babbar dama ga Nijeriya a bangaren kere-kere.
“Zai iya zama jagora a fasahar kera jiragen sama da kayayyakin tsaro,” a cewar Malam Auwal Ibrahim Shehu, Daraktan kungiyar Haske Peace Debelopment Initiatibe, wata kungiya mai zaman kanta da ke Kaduna.
Malam Yunusa ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa a kan baiwarsa, duk da matsalolin da yake fuskanta.
Yunusa ya ce, “Na san ina da wata baiwa mai amfani. Abin da kawai nake bukata shi ne dama domin in nuna duniya abin da zan iya yi.”
Ko labarinsa zai zama nasara a gare shi da kasar gaba daya, ko kuma baiwarsa zata watse, hakan ya dogara ne da yadda Nijeriya za ta dauki mataki a kan lamarinsa.