Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Filato
Published: 14th, March 2025 GMT
Jami’an tsaro a Jihar Filato, sun ceto mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace.
An gano mutanen a yankin Ganawuri, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, bayan da sojojin Operation SAFE HAVEN (OPSH) suka kai farmaki maɓoyar ’yan bindigar.
Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-RufaiAn gudanar da aikin ceton ne a matsayin wani ɓangare na Operation LAFIYAN JAMA’A, wanda ke da nufin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa sojojin sun samu bayanan sirri cewa an ɓoye wasu mutane da aka sace a kusa da hanyar Jos zuwa Ganawuri.
“Yayin farmakin, sojojinmu sun yi arangama da ‘yan bindigar, amma sun tsere bayan sun fuskanci ruwan wuta.
“Daga nan, sojojin suka bi sahu suka kuma ceto mutum bakwai da maharan suka sace,” in ji Manjo Zhakom.
An bayyana sunan mutanen da aka ceto, waɗanda dukkaninsu ‘yan asalin Jihar Bauchi ne: Sale Umar, Muhammadu Inusa, Abdullahi Abdulrasaq, Abdulsalam Muhammad, Muhammad Hamisu, Ibrahim Maradu, da Saidu Sani.
Sojojin sun kuma gano wata jaka mai ɗauke da bargo da kaya da ‘yan bindigar suka bari.
Sun yi wa mutanen da suka ceto tambayoyi don taimakawa musu da bayanan da za su sa a kama ‘yan bindigar da suka tsere.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan bindigar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje fiya da 10 a yankin Biyabiki da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
’Yan ta’addan sun cinna kona wuraren ne bayan sallar Isha’i a ranar Asabar a wani da ake zargin na ramuwar gayya ne kan kashe Isuhu Yellow, kanin wani jagoran ’yan bindiga mai suna Adamu Aliero.
Shaida sun ce da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindiga Adamu Aliero ne suka kai harin a kan babura, inda suka banka wa wuraren wuraren wuta, sannan suka tsere ba tare da taba mazauna ba.
“Wuraren da suka cinna wa wuta sun hada da masallacin Juma’a da wani karamin asibiti da kuma gidaje kimanin 10 da suka lalata,” in ji wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa.
A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a MajalisaAna kyatuta zaton harin na da alaka da kashe Adamu Yelow a wani harin kwanton bauna da shi da tawagarsa suka kai wa jami’an tsaro, a yankin Keta, kimanin makonni uku da suka gabata, amma jami’an tsaron suka aika su lahira.
Tun da farko a ranar sai da ’yan ta’addan sun kuma kai wani hari a kauyen Tsageru a ranar, inda suka kona gidaje da dama.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Ba mu san wace butaka suke neman cim ma da kona gidaje da kayan gwamnati da suke yi ba; Tun da aka kashe Isuhu Yellow yankunanmu ke ta fuskantar barazana, don haka muna kyatata zaton wanna harin ramuwar gayya ce.”
Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da kakakin ’yan sanda na Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, domin samun karin bayani, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, bayan ya yi ta kiran wayar jami’in.
Wannan hari na kara nuna alamr ci gaban matsalar tsao a Jihar Zamfara inda ’yan bindiga ke kara cin karensu a yankunan karkara, duk kuwa da kokarin hukumomin tsaro na yi wa tufkar hanci a yankin.