Matawalle Ya Ba Magoya Bayan APC Na Zamfara Naira Miliyan 500
Published: 14th, March 2025 GMT
Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.
A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.
Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.
“A wannan karon, maimakon ba wa jama’a hatsi iri-iri, Ministan ya yanke shawarar bayar da tsabar kudi saboda wasu ‘yan siyasa sun riga sun raba kayan abinci,” ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa, tsohon Gwamna Sanata Abdul Aziz Yari ya bayar da gudummawar tireloli na hatsi iri-iri 496, wanda hakan ya sa Ministan ya kara wannan kokari da tallafin kudi.
Gidan-Goga ya bayyana cewa, mutane 200 daga kowace karamar hukuma 14 da ke Zamfara sun karbi ₦100,000 kowanne, wanda ya kai miliyan 280.
“Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC 24 daga kananan hukumomi biyar na shiyyar Sanatan Zamfara ta Yamma sun karbi ₦250,000 kowanne, wanda ya kai miliyan 30.”
“Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC 90 daga kananan hukumomin jihar Zamfara ta tsakiya da kuma ta Zamfara ta Arewa sun karbi ₦250,000 kowanne, wanda ya kai miliyan 22.5.”
Sauran nau’ikan wadanda suka ci gajiyar kuma sun sami kudade a matsayin wani bangare na kunshin jin dadin Ramadan na Minista.
Gidan-Goga ya tabbatar da cewa sama da kashi 80 cikin 100 na wadanda aka yi niyya sun karbi kudadensu.
Ya lura cewa wadanda suka amfana daga Bakura, Gummi, Kaura-Namoda, Maradun, Shinkafi, da Talata-Mafara duk sun tattara kudadensu.
Sai dai kawo yanzu mutum 100 da suka ci gajiyar tallafin daga kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Bungudu, Bukkuyum, da Anka ne kowannensu ya karbi nashi kason, yayin da sauran wadanda suka ci gajiyar shirin za a biya su nan gaba kadan.
Ya kara da cewa har yanzu wadanda suka ci gajiyar tallafin daga karamar hukumar Birnin Magaji ba su samu kudadensu ba sakamakon tsaikon da aka samu wajen gabatar da jerin sunayen wadanda suka karba.
AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Matawalle Zamfara da suka ci gajiyar wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
Pakisatan: An Kubutar Da Mutane 155 Sannan Yan Ta’adda 27 Suka Halaka A Garkuwan Jirgin Fasinja A Jiya Talata
Jami’an tsaro a kasar Pakistan sun kubutar da mutane 155 daga cikin fasinjoji kimani 450 wadanda yan bindigan daga kungiyar ‘Baloch Liberation Army (BLA) suke garkuawa da su tun jiya, wadanda suka yi barazanar kashesu, idan gwamnatin Islamabad bata biya masu bukatunsu ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar jami’an tsaro na kasar ta Pakisatan na cewa ya zuwa yanzu sun halaka yan bindiga 27. Sannan suna shirin kubutar da sauran nan gaba. Labarin ya kara da cewa daga cikin wadanda aka kubutar akwai mata da yara.
Kafin haka dai a jiya Talata ce yan bindiga na kungiyar BLA suka tsare wani jirgin fasinja mai suna ‘Jaffar Express’ dauke da fasinjoji 450 daga garin Quetta zuwa Peshawar.
Manufar garkuwan dai ita ce neman gwamnatin Pakisatn ta bawa yankin Baluchistan na kasar Pakisatan yencin kanta a matsayin kasa mai zaman kanta.
Labarin ya ce yan bindigan sun ta da nakiya ne suka lalata layin dogon, kafin su tilastawa Jirgin tsayawa.
Ya zuwa yanzu dai yan bindigan sun kashe mutane 3 daga cikin har da direban jirgin.