Gwamnatin Jihar Kano Ta Kebe Filin Gina Hedikwatar NWDC
Published: 14th, March 2025 GMT
Hukumar raya yankin arewa maso yamma NWDC ta bukaci gwamnatocin jihar Kano da su taimaka tare da hadin gwiwa da nufin cimma manufofinta.
Shugaban Hukumar Alhaji Isma’il Lawal Abdullahi Yakawada ya nemi hadin kan a lokacin da ya jagoranci mambobin hukumar a ziyarar ban girma da suka kai wa gwamnan a gidan gwamnatin Kano.
Ya ce hukumar ta NWDC na da burin tabbatar da ci gaba da bunkasar jihohin Arewa maso Yamma, tare da mai da hankali wajen magance matsalolin da suka addabi kasa kamar rashin tsaro, yunwa, fatara, da rashin abinci mai gina jiki.
Ya nemi goyon bayan da ake bukata da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano domin cimma aikin da ke gabansa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan kafa hukumar NWDC, inda ya yaba da matakin sanya hedikwatar hukumar a Kano ba tare da la’akari da harkokin siyasa ba.
Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na tallafawa manufofin hukumar, tare da amincewa da kafa hukumar ta NWDC a kan lokaci domin tunkarar kalubalen da yankin ke fuskanta.
“Mun riga mun samar da filin da ya dace wanda zai yi aiki don gina ofisoshin wannan hukuma mai daraja.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa, yankin Arewa maso Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makami, da sauran ayyukan muggan laifuka.
” Ana sa ran kafa hukumar ta NWDC zai taimaka wajen magance wadannan al’amura, da inganta ci gaban tattalin arziki, hadin kan al’umma, da inganta rayuwar jama’a.”
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Jarida Muhimman Ginshiƙai Ne A Tsakanin Al’umma Da Gwamnati – Gwamnatin Nasarawa
Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule.
Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar.
Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su, domin tabbatar da sahihanci da ingancin aikin jarida.
Da yake ƙarin bayani, ya ce gwamnatin Abdullahi Sule ta kawo sauye-sauye masu amfani, musamman wajen inganta harkar haƙar ma’adinai a jihar.
Ya bayyana cewa Jihar Nasarawa ce ke kan gaba a Naieriya wajen samar da ma’adinan Lithium, wanda ke amfani ga ci gaban tattalin arziƙi.
A nasa jawabin, Shugaban ‘Yan Jarida na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya sabon Sakataren Gwamnatin Jihar murna bisa naɗin da aka yi masa.
Ya ce naɗin da aka yi wa Labaran Shuaibu Magaji ya dace da shi, kuma ‘yan jarida ba su yi mamaki ba duba da irin tarihin ayyukansa.
Haka kuma, ya roƙi Sakataren Gwamnatin da ya haɗa su cikin harkokin yaɗa labarai na gwamnati, musamman a ɓangaren tallafa wa ayyukansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp