Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan

 

Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.

 

Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da matasa a cikin watan Ramadan da bayar da tallafi mai mahimmanci.

 

Olawande, wanda ya samu rakiyar Seyi Tinubu, ya jaddada mahimmancin shirye-shiryen da suka shafi matasa, ciki har da samar da dandalin tattaunawa kan ci gaban matasa na kasa.

 

Ya yi nuni da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu suna da manufa daya na ci gaban matasa, ta yadda za a yi amfani da albarkatun da aka ware wa Sokoto yadda ya kamata.

 

Ministan ya kuma yaba da bullo da shirin ba da lamuni na dalibai, inda ya bayyana shi a matsayin wani gagarumin shiri na tallafawa daliban Najeriya.

 

Ya kuma ba da tabbacin cewa, akwai wasu shirye-shiryen da suka shafi matasa, inda Sokoto za ta ci gajiyar muhimman tsare-tsare a fannin noma, gidaje, da kuma shirye-shiryen horarwa.

 

Ya kuma kara ba da tabbacin cewa FG na kokarin samar da yanayi mai dacewa da matasan Najeriya za su ci gaba.

 

A nasa jawabin, gwamna Ahmed Aliyu na sokoto, ya bayyana ziyarar a matsayin wata shaida ga jajircewar da gwamnatin ta yi wajen karfafa matasa.

 

Ya yabawa Seyi Tinubu, wanda shine wanda ya assasa Renewed Hope Youth Empowerment Initiative, bisa gudunmawar da yake bayarwa a harkokin siyasa da ci gaban tattalin arziki, yana mai kira gare shi da ya mika shirye-shiryensa ga matasan Sokoto.

 

Gwamnan ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin sa ke yi na tallafa wa matasa da suka hada da nada matasa a manyan mukamai a gwamnati da samar da ilimi kyauta ga dukkan dalibai ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

 

Ya yabawa Tinubu kan irin ayyukan alheri da yake yi a cikin watan Ramadan, musamman ga marasa galihu.

 

Tun da farko, Seyi Tinubu ya bayyana kudirinsa na ci gaban matasa a Sakkwato, inda ya yi alkawarin cewa gidauniyarsa za ta ci gaba da tallafa wa ayyuka a fadin kananan hukumomin jihar 23.

 

Nasir Malali

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Karfafa Huldar Dake Tsakaninta Da Kano

A cewar Dunbai, gwamnatin kasar Sin tana kara inganta alakarta da jihar Kano a fannonin samar da abinci, kayayyakin more rayuwa, ilimi, tare da kasuwanci da gwamnatin jihar.

 

A fannin aikin gona, wakilin kasar Sin ya yi nuni da muhimmancin samar da abinci a jihar Kano, inda ya ce, jihar da ke da dimbin al’umma kamar kasar Sin, ta cancanci amfani da fasahohin zamani a fannin noma don karfafa samar da dimbin abinci.

A cikin sanarwar, Mista Dunhai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ci moriyar damar da kasar Sin ta samar na zuba jari a Nijeriya na sama da dala tiriliyan 20, domin farfado da ci gaban masana’antu da kasuwanci.

 

A nasa jawabin, Gwamna Yusuf, wanda ya tarbi tawagar jama’ar Sinawa da hannu biyu, ya kara da cewa, a shirye gwamnatinsa ta ke ta kara himma wajen hadin gwiwa domin ci gaban jihar baki daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3
  • Ƙasar Sin Ta Yi Alƙawarin Ƙarfafa Hulɗar Da Ke Tsakaninta Da Kano
  • Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Karfafa Huldar Dake Tsakaninta Da Kano
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar
  • Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
  • Gidauniyar Bafarawa Ta Rabawa Kananan ‘Yan Kasuwa Naira Milliyan 13 a Sokoto
  • Tambuwal Ya Raba Shinkafa Ga Gidaje Dubu 30 A Sokoto
  • Gwamnan Zamfara Ya Haɗa Kai Da Kamfanonin Sin Don Habaka Tsaro
  • Gwamna Buni Ya Naɗa Matasa 200 A Matsayin Hadimansa