Likitoci Sun Shawarci Jama’a Su Rika Zuwa Asibiti Akai-Akai
Published: 14th, March 2025 GMT
Babban magatakarda, sashin Nephrology, Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga ya bukaci jama’a da su rungumi salon rayuwa mai inganci domin hana kamuwa da cutar koda.
Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Gombe a yayin bikin ranar ciwon koda ta duniya.
Dokta Fidelis Linga ya bayyana halaye marasa kyau kamar yawan shan barasa, shan taba, cin abinci mara kyau, da kuma salon rayuwa a matsayin abubuwan da ke haifar da hauhawar cututtukan da ke da alaƙa da koda.
Ya kuma jaddada mahimmancin ziyarar asibitoci akai akai, da daidaita tsarin abinci, da motsa jiki a kai a kai wajen hana kamuwa da cutar koda.
Ya bayyana cewa a duniya baki daya, mutane miliyan 850 ne ke fama da cutar koda wanda miliyan 11 daga ciki ke mutuwa daga cutar a duk shekara yana mai bayyana yanayin a matsayin abin damuwa.
Dokta Fidelis Linga ya ce FTH Gombe na kokarin samar da karin injinan wankin koda wato dialysis da ma’aikatan lafiya don biyan bukatun dimbin masu cutar koda da ke zuwa wurin aikin wankin.
Ya ce an yi ƙoƙarin ne don inganta hanyar yin amfani da dialysis na ceton rai ga majinyata da ke fama da cututtukan koda.
HUDU Shehu/Gombe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
A ranar Juma’a da daddare, wata fashewar bama-bama a wata shahararriyar kasuwa a titin Kodesoh, Ikeja dake Lagos ta janyo raunuka ga mutane da dama. Shaidu sun bayyana cewa fashewar ta faru ne lokacin da wani mai kula da shagon kyamara ya yi kokarin bude wani kunshin da aka kawo.
Hukumar agajin gaggawa, tare da jami’an ‘yansanda daga tashar yankin G, EOD-CBRN Base 23 ta Ikeja, da ma’aikatan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Lagos (LASTMA), sun tura jami’ansu domin gudanar da ayyukan daukar matakai da tsaro a wurin.
Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A YauWani shaida gani da ido, Lucky Okoro, ya bayyana yadda ya samu damar gudu wa daga wurin fashewar, yana mai cewa, “kawai nayi ƙoƙarin shiga shagon, sai fashewar ta afku. Ban jima ba, sai na ga wutar tana kona wani mutum da wata mata a cikin shagon.” Wani shaidar, Olumide Gbeleyi, wanda yake daga wani otel kusa da wurin, ya bayyana cewa, “Mun ji hayaniyar fashewar kuma muka ga hayaki ya rufe ko’ina. Wata mata tana sayar da kayan ciye-ciye a waje ta ji rauni mai tsanani.”
Sule Aminu, wanda ya bayyana yadda abin da ya sani game da lamarin, ya zargi cewa kunshin mai ban mamaki yana dauke da wani abu da aka tura domin cutar da mai shagon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp