‘An Kwashe Shekaru Ana Kashe Kudaden Yaran da ba a ma Haife su ba a Nijeriya’
Published: 14th, March 2025 GMT
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa.
Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya kasar na kashe kudaden yaran kasar da ba a kai ga haihuwarsa ba.
“Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kudaden yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kudin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce.
Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama’a.
“Mun fuskanci tarin kalubale a lokacin da na karbi mulki. Inda ba mu dauki matakai ba da yanzu kasar ta talauce, kuma ai hakkinmu ne mu kare tattalin arzikinmu daga rugujewa”, in ji Shugaba Tinubu.
To amma shugaban ya ce a yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dangane da sauye-sauyen da gwamatinsa ta fara ɓullo da su.
“Amma a yau bayan shimfida mai kyau da muka yi, mun smau nasarar magance matsalolin da suka tunkaro kasarmu, a yanzu canjin kudi ya daidaita, farashin abinci na ci gaba da sauka, musamman a lokacin Ramadan, da yardar Allah wahalar ta zo karshe”, a cewar shugaban kasa.
Bello Wakili/Abuja
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo
A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar.
Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas.
Sauran yan takarar sun hada da Firaministan kasar Alain Claude Bilie-by-Nze, wanda ya rike wannan mukami a lokacin mulkin Bongo, da kuma wasu manyan kusoshin tsohuwar jam’iyya mai mulki ta PDG.
Kimanin mutum miliyan daya ne aka tantance su kada kuri’a a zaben, daga cikin jimilar miliyan biyu da rabi na kasar.
A karfe 06:00 na yamma agogon kasar wato 05:00 na yamma agogon GMT, na yau aka tsara rufe rumfunan zaben.
Za a iya fara sanar da sakamakon zaben daga gobe Lahadi.