Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
Published: 14th, March 2025 GMT
A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa.
Haka nan kuma sun ce; Tuntubar juna da kuma tattaunawar diplomasiyya bisa girmama juna ne kadai zabin da ake da shi domin cimma manufa.
Taron da aka yi a yammacin birnin Beijing ya kunshi mataimakan ministan harkokin wajen Iran Garid Ridh Abadi, Sai Rasha Sergey Ryabkov da kuma mai masaukin baki na China Ma Zhaoxu.
A daya gefen kasashen uku sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu a karkashin kungiyoyin kungiyoyin “Shanghai” da kuma “Brikcs”.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar.
Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar.
Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko.
Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su ka yi, har sau uku a cikin shekarar hijira Shamshiyya ta 1403. Sannan da wadanda za su a sabuwar shekara da za ta shigo.
Ya ce za’a gudanar da wani atisayen wanda zai da ce da girman barazanar da ake fuskanta.
Haidari ya kammala da cewa a sabuwar shekarar Iran da za a shiga, za ta zama ta kara yawan karfin tsaron kasar ne, domin takawa makiya birki.