HausaTv:
2025-03-14@14:50:22 GMT

 An Yi Gargadi Akan Rushewar Kungiyar  Agajin Falasdianwa Ta UNRWA

Published: 14th, March 2025 GMT

Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu.

Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.

Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi.

Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai  HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da duk wani aiki da ita.

MDD ce dai ta kafa wannan kungiyar domin taimakawa Falasdinawan da kirkirar HKI ya yi sanadiyyar mayar da su ‘yan gudun hijira.

Wasu kasashe da kuma kungiyoyi da dama a duniya sun yi tir da matakin na HKI da kuma Amurka akan wannan kungiya.

Da akwai yaran Falasdinawa 100,000 a cikin Gada kadai da suke karatu a karkashin makarantun kungiyar.

Philippe Lazzarini ya ce, idan aka hana wadannan yaran karatu to mun shuka irin tsattsauran ra’ayi, wanda zai zama babban bala’i.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%

Yau ce ranar dasa bishiyoyi ta kasar Sin, kuma albarkacin ranar ofishin kwamiti mai kula da harkokin dasa bishiyoyi na Sin ya gabatar da sanarwar karuwar yawan bishiyoyi da Sin ta dasa, wadda ta nuna cewa, Sin ta gabatar da manyan tsare-tsaren kiyaye muhalli, don daidaita harkoki masu nasaba da hakan a shekarar 2024, inda aka samu ci gaba mai armashi a bangaren dasa bishiyoyi.

Sanarwar ta nuna cewa, a wannan shekara Sin ta dasa itatuwa hekta miliyan 4.446, da ciyayi hekta miliyan 3.224, da kuma daidaita kasa mai rairayi hekta miliyan 2.783, hakan ya sa yawan fadin gandun daji ya kai kashi 25%.

Tun lokacin da aka kira taro karo na 18 na jam’iyyar JKS, hukumar lura da itatuwa da ciyayi ta Sin ta aiwatar da manyan ayyukan dasa bishiyoyi da habaka fadin gandun daji, da kyautata ingancin itatuwa da kiyaye albakatun bishiyoyi. Yawan itatuwa da Sin ta dasa a wurare masara shuke-shuke ya kai hekta miliyan 77.33, hakan ya sa Sin ta zama kasa mafi samun ci gaba wajen dasa bishiyoyi. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10
  • Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
  • FERMA Ta Sake Jaddada Sadaukarwar Da Take Yi Na Kula Da Hanyoyin Tarayya
  • Hamas ta yi maraba da matakin Yemen na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga teku
  • Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%
  • Kungiyar Tarayyar Turai ta yi barazanar sake kakaba wa Syria takunkumi
  • Yemen zata sake kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila
  • Hamas : matakin Isra’ila na hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza ”laifi na yaki”ne
  • ’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan