HausaTv:
2025-04-14@17:37:28 GMT

Karancin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Yana Damun ‘Yan Kasa

Published: 14th, March 2025 GMT

An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa.

Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum.

Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa.

Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan.

Su kuwa matukan motocin Tasi (SYNCTAXITU), cewa su ka yi, ya kamata gwamnati ta kara yawan man fetur da ake hakowa a kowace rana.

Babban sakataren kungiyar matuka Tasi din Agali Ibrahim cewa ya yi, “ Idan aka fada mana cewa da akwai manyan motocin jigilar man fetur 25 da ake bai wa birnin Niamey, to abinda zan fada musu shi ne cewa bai isa ba.”

Haka nan kuma ya yi ishara da fasakwaurin man fetur din da ake yi da yana daga cikin dalilin karancinsa da ake fuskanta.

Da akwai shirin kara yawan tankokin mai daga 25 zuwa 100 da za a rika bai wa babban birnin ka kowace rana.

Ba kasafai ake shiga irin wannan yanayin ba a jamhuriyar Nijar wacce take da arzikin mamn fetur da aka fara hako shi tun a wajajen 2011.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi

Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa.

A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin arziki da gobarar tankar mota da ambaliyar ruwa da gobara, abin da yake biyo baya shi ne gwamnati ta raba tallafin shinkafa da sauaran kayan abinci, tamkar shinkafa ita ce maganin duk wata matsala. A wasu lokutan, a kan raba babura masu kafa uku da dabbobi a matsayin tallafi.

Makudan kudaden da gwamnatoci suke kashewa da sunan bayar da tallafi, inda ba a ganin tasirin hakan a rayuwar ’yan kasa, lamari ne da ke ci gaba da damun ’yan Nijeriya. Alal misali, makudan kudaden da gwamnatocin jihohi arewa suka ware da sunan ciyarwar watan Ramadana ya saha suka daga ’yan kasar da dama, cikinsu har da masu amfana da ciyarwar.

A yayin da Gwamnatin Jigawa ta sanar da kashe Naira biliyan 4.8, ita kuwa Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8 domin ciyarwar Ramadanan 2025. Gwamnatin Sakkwato ta ware Naira biliyan 6.7, yayin da Gwamnatin Kebbi ta ware Naira biliyan 1.5, inda Gwamnatin Neja ta ware Naira miliyan 976. A nata bangaren, Gwamnatin Yobe ta ware Naira miliyan 298. Uwa-uba, Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 10 duk don ciyarwar watan Ramadana.

Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa

Damuwar da masu ruwa da tsaki suka bayyana ita ce yadda gwamnatocin suka kashe wadannan makudan kudade da sunan shirin ciyarwar Ramadana. Misali, shirin ciyarwar Gwamnatin Jigawa an yi hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar da kananan hukumomi bisa kaso 55 da 45. Rashin tabbacin da ke tattare da wannan shiri shi ne su wane ne ainihin wadanda suka amfana da wannan shiri na ciyarwa, sannan kuma wanne tsari aka bi wajen rabo?

A wata ziyar ba-zata da Gwaman Jihar Jigawa ya kai daya daga wuraren ciyarwar a karamar Hukumar Dutse a Ramadanan da ya gabata, ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da tsarin da ya gani, wanda hakan ya tabbatar da sukar da al’umma suke yi a kan rashin tsarin shirin ciyarwar. Gwamna Namadi ya nuna rashin amincewarsa game da rashin tsari da karancin abincin a cibiyoyi 609 da aka tsara za su bayar da abinci kala uku ga masu rauni da talakawa 182,700 a kullum. Ya koka da cewa, ‘‘Ban gamsu ba, kodayake ban yi mamaki ba da rashin tsari da sakacin da na gani ba a yau. Ba zai yiwu ba wasu ’yan tsiraru su hana mutanenmu amfana da abin da suka cancanci su samu ba.’’

Duba da irin yadda aka tafiyar da shirin ciyarwar Ramadana, shirin cike yake da almubazaranci da kudin al’umma. Rashin tartibiyar hanyar tabbatar da wadanda suka amfana da shirin, ita ce ta ba wa cin-hancin kofar shigowa. Wannan wata sabuwar hanyar satar kudin al’umma ce cikin sauki da sunan bayar da tallafi, da ya kunshi ciyar da masu rauni a watan Ramadana.

A yayin da ba za a sa kafa a shure irin rawar da bayar da tallafin gwamnati yake takawa ba a yanayi na gaggawa, masu rauni da talakawa za su fi amfana, idan aka saka wadannan makudan kudade a harkar noma da samar da aikin yi ga matasa da mata da samar da kanan masana’antu, wadanda za su samar da mafita ta dindindin. Gwamnati ta yi wa bayar da tallafi mummunar fahimta, duba da yadda ta ba shi muhimmanci, wanda hakan ke nuna dalilin da ya sa aka kasa warware matsalolin kasa yadda ya kamata.

Ya kamata bayar da tallafi ya zamto saboda wasu dalilai na musamman, da nufin bayar da agaji na wucin-gadi, ba samar da mafita ta dindindin ba ga muhimman matsalolin kasa kamar talauci da rashin aikin yi ba. Ana bayar da tallafi ne ga mutanen da suke cikin yaki kamar a yankin Sudan da Gaza.

Shugabanni, musamman gwamnonin jihohi sun fi fifita raba tallafi a al’amuansu na gwamnati, ta yadda kusan ya zama wata hanya ta kimanta ayyukan zababbun masu rike da mukaman gwamnati, duk dai saboda sun gaza fahimtar yadda ake kimanta matsayin tattalin arzikin mutane, wanda ya hada da talauci da tallafi.

Ware makudan kudade domin ciyarwar watan Ramadana ba ita ce hanyar da ta dace ba wajen shawo kan matsalar tattalin arziki da ’yan kasa suke fuskanta. Samar da mafita ta wucin-gadi ko bayar da tallafi ta hanyar ciyarwa ko raba babura ba ita ce tartibiyar hanyar shawo kan matsalar ba. Ana yakar talauci da rashin aikin yi ne ta hanyar ba wa ’yan kasa horo, ba tallafin kaya ba.

Babu wata kasa da ta ci gaba ta hanyar raba kayan tallafi. Shugabanni suna cutar ’yan Nijeriya ne ta hanyar fifita bayar da kayan tallafi, da nufin yin awon gaba da kudin al’umma, wadanda sun isa su samar da mafita ta dindindin ga matsalolin zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya.

Bisa ga irin dimbin arzikin da kasar nan take da shi, da ya hada da yawan mutane, wadda wata dama ce ta rage talauci da rashin aikin yi, inda ’yan Nijeriya, musamman matasa suke bukatar horo fiye da raba kayan tallafi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Zata Yaye Labulen Ire-Iren Makamanta Na Musamman Da Ta Mallaka Domin Kare Kai
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
  • Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
  • Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
  • Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo
  • Tsohon Kocin Super Eagles, Christian Chukwu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 74
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 108