Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
Published: 14th, March 2025 GMT
Jihohin Sakkwato da Kebbi na fuskantar ƙalubale sakamakon cutar sanƙarau da ta ɓulla a jihohin, inda rahotanni suka tabbatar da cewa cutar ta kashe aƙalla mutum 50, yayin da sama da mutum 200 suka kamu da cutar.
A Jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu ne suka fi fuskantar matsalar, inda cutar ta fara yaɗuwa kafin a ɗauki matakan gaggawa.
A Jihar Sakkwato kuwa, ƙaramar hukumar Tambuwal ce ta fi fama da cutar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka sanar da ɗaukar matakan daƙile cutar domin hana ta yaɗuwa zuwa sauran yankunan.
Dalilin Yawaitar CutarMasana kiwon lafiya sun danganta yawaitar cutar da tsananin zafi da ake fama da shi a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ke haifar da bushewar iska da kuma saurin bazuwar ƙwayoyin cutar sanƙarau.
Rashin isassun matakan rigakafi da kuma ƙarancin kula da lafiyar jama’a a wasu yankuna na daga cikin dalilan da suka sa cutar ke bazuwa cikin sauri.
Matakan da Aka ƊaukaGwamnatocin jihohin Kebbi da Sakkwato sun ce sun fara ɗaukar matakan gaggawa, inda ake gudanar da allurar rigakafi domin daƙile cutar, musamman ga ƙananan yara da tsofaffi, waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.
Hakazalika, an ƙara wayar da kan jama’a kan alamomin cutar da matakan kariya, domin daƙile yaɗuwarta a cikin al’umma.
Abubuwan da Jama’a Ke BuƙataDuk da matakan da hukumomi ke ɗauka, har yanzu jama’a na buƙatar ƙarin taimako, musamman wajen samun ingantattun cibiyoyin lafiya da isassun magunguna.
Akwai buƙatar gaggauta aika ƙarin kayayyakin kula da lafiya da ƙarfafa rigakafi domin hana aukuwar cutar a nan gaba.
A halin yanzu, hukumomin lafiya na ci gaba da sa ido kan lamarin, tare da jan hankalin jama’a da su guje wa cunkoso da kuma kai marasa lafiya asibiti da wuri idan suka fara ganin alamomin cutar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: lafiya Sakkwato Sanƙarau
এছাড়াও পড়ুন:
Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu.
Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar ranar Laraba.
Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a KatsinaSansanin ya tanadi waɗanda suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke, da Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin inda wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari a ranar Asabar ɗin da ta gabata, inda suka kashe mutum 11 tare da ƙona gida ɗaya daga cikin ƙauyukan.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Yahaya Sarki ya fitar, ta ce Gwamna Idris ya kai ziyarar ne domin jajanta wa mutanen tare da ganewa idonsa halin da suke ciki, domin sanin matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka.
Idris wanda ya bayyana alhininsa kan asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, ya yaba wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi na shawo kan rikicin.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake yawan samun hare-haren daga Jihar Sakkwato da ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar.
“Na yaba wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa bisa gaggauta kafa sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda na umarce shi.