Aminiya:
2025-04-14@16:18:07 GMT

Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar

Published: 14th, March 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Arewa domin inganta tsaro.

Ya yi wannan roƙo ne bayan ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira a Kangiwa, bayan harin da wasu da ake zargin Lakurawa ne suka kai musu.

Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3

Harin da aka kai a ranar 9 ga watan Maris ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da ƙone ƙauyuka bakwai.

Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro, da Garin Rugga.

“Sansanin soji a yankin zai taimaka wajen gaggauta kai ɗauki idan an kai wani hari,” in ji Gwamna Idris.

“Dole mu yi duk abin da za mu iya don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Yayin ziyarar tasa, gwamnan ya yi alƙawarin taimakawa wajen sake gina gidajen mutanen da suka rasa matsugunansu.

Haka kuma, ya umarci hukumomin ƙaramar hukumar da su riƙa samar wa ’yan gudun hijirar abinci, tare da yanka saniya bayan kwana huɗu.

Bugu da ƙari, ya umarci a yanka raguna biyu don jarirai huɗu da aka haifa a sansanin yayin rikicin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa, Alhaji Sani Aliyu, ya gode wa gwamnan bisa ƙoƙarin da yake yi.

“Gwamnatin jiha tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar tsaro, amma muna buƙatar ƙarin tallafi daga Gwamnatin Tarayya,” in ji shi.

Gwamnan ya buƙaci mutanen da abin ya shafa da su ci gaba da haƙuri da addu’a, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnati na ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamna Lakurawa Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya

A kowane wasa, tauraron Super Eagles Iwobi na nuna cewa ba wai kawai tarihi yake son kafawa a Duniya ba, ya na sake rubuta labarin ‘yan wasan kwallon kafar Nijeriya a Turai, shan kayen da Liverpool ta yi a Craben Cottage ya jinkirta damarta na lashe gasar Firimiya Lig ta bana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Bada Ai hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Siyo Tan Tan 360 Ga Manoma
  • Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • Idris Ya Musanta Rahoton Wai Ya Ce A Yi Watsi Da Koken Gwamna Zulum Kan Rashin Tsaro A Borno