Gwamnatin Jigawa Da Bankin Duniya Sun Dauki Nauyin Dalibai 500 A Fannin Fasahar Zamani
Published: 14th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta dauki nauyin dalibai sama da 500 a wani mataki na tsara makomar matasa a fannin fasahar zamani.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin da kuma mika takardun shaidar karatu ga wadanda suka ci gajiyar shirin fasahar zamani na Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) a Jihar Jigawa.
Malam Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafawa matasa ta hanyar kirkire-kirkire a fannin fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki.
“A yau, mun kammala horar da dalibai 240 da suka koyi yadda za su bunkasa harkokinsu na kasuwanci don tabbatar da ci gaba mai dorewa,” in ji gwamnan.
“Haka kuma, a yau muna mika takardun shaidar karatu ga dalibai 550 da suka sami guraben karatu ta hannun Hukumar Samar da Ayyuka da Taimakon Matasan Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, Arms of Ideas, da gwamnati.”
A cewarsa, wadannan dalibai da suka sami guraben karatu a Jami’ar Baze za a horas da su a fannonin fasahar zamani da ke taka muhimmiyar rawa a kasuwannin duniya.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa karkashin wannan shiri, Gwamnatin Jihar Jigawa da Bankin Duniya sun saka hannun jarin sama da Naira miliyan 100 domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi da koyon sana’o’i.
“Wannan kudade hadin gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya da Gwamnatin Jihar Jigawa. Bankin Duniya ya bayar da Naira miliyan 85, yayin da gwamnatin jihar ta bayar da Naira miliyan 50, kuma an riga an biya kudaden gaba daya.”
Ya kara da bayanin cewa shirin zai ba dalibai damar koyon akin binciken sirri, (Artificial Intelligence), da fasahar blockchain, binciken kasuwanci (Business Intelligence), da tsaron yanar gizo (Cybersecurity), da sauransu.
Baya ga horon fasahar zamani, gwamnan ya kuma sanar da kammala horas da matasa ‘yan kasuwa 240 da suka samu horo kan hanyoyin bunkasa kasuwancinsu. Ya kara da cewa kowannensu zai samu tallafin jari na Naira 50,000 domin fadada kasuwancinsu da kuma tabbatar da dorewarsa.
Saboda haka, Gwamna Namadi ya bukaci daliban da su yi amfani da wannan dama yadda ya kamata, tare da tabbatar musu da karin tallafi ga wadanda suka yi fice a karatunsu.
“Ina bukatar ku yi kokari don cimma wannan buri. Duk wani dalibi da ya kammala karatu da Upper Credit ko Distinction zai samu sabuwar kwamfutar tafi-da-gidanka (laptop) domin tallafa masa!”
Ya sake tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa ga fannin fasahar zamani, da karfafawa matasa tattalin arziki a Jihar Jigawa, tare da alkawarin gabatar da karin manufofi da shirye-shirye don inganta rayuwarsu da kuma bunkasa sana’o’insu.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bankin Duniya Jigawa Gwamnatin Jihar fasahar zamani Bankin Duniya Jihar Jigawa tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Ai hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
Gwamnatin jihar Jigawa ta bada kwangilar sanya kwalta akan hanyar Dolen kwana zuwa Garin Gabas zuwa Hadejia, kan naira miliyan dubu bakwai da miliyan dari takwas.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da aikin sanya kwaltar.
Ya ce aikin hanyar mai tsawon kilomita 29, ana sa ran kammalawa nan da watanni 12 masu zuwa.
Malam Umar Namadi ya kara da cewar, an bada aikin sanya kwaltar ne da kuma sauran ayyukan inganta hanyoyi domin saukakawa manoma da sauran al’umma harkokin sufuri.
A don haka, ya yi kira ga al’ummar jihar da su rinka sa ido akan kayayyakin da hukuma ta samar musu domin gudun lalacewa da kuma barnatarwa.
A jawabinsa na maraba, kwamishinan ayyuka na Jihar, Injiniya Gambo S Malam ya ce gwamnatin jihar, ta bada ayyukan hanyoyi 47 masu nisan kilomita 800 a sassan jihar.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, bikin ya samu halartar Ministar ma’aikatar Ilmi Dr. Suwaiba Ahmed Babura da Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori da kakakin majalissar dokokin jihar Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da manyan jami’an gwamnatin jihar.
Usman Mohammed Zaria