Birnin Beijing Ya Shirya Yiwa ‘Yan Mata Rigakafin Cutar HPV Kyauta
Published: 14th, March 2025 GMT
Mahukuntan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun sanar da shirin fara yiwa ’yan mata dake makarantun karamar sakandare allurar rigakafin cutar HPV, mai haifar da karin bakin mahaifa kyauta, tun daga watan Satumban bana, a wani mataki na dakile karuwar mata dake kamuwa da cutar.
A cewar sanarwar hadin gwiwa ta cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta birnin da sauran hukumomi masu alaka da aikin, wadda aka fitar a jiya Alhamis, ya zuwa karshen watan nan na Maris, ’yan mata da a yanzu haka ke ajin karshe na makarantun firamare, za su cike takardun amincewa da karbar rigakafin, kana ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, za a kammala yi musu kashin farko na rigakafin.
An shirya gudanar da rigakafin ne domin amsa kira, ga shirin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta kaddamar, wanda ke da nufin tabbatar da cewa ya zuwa shekarar 2030, kaso 90 bisa dari na ’yan matan da suka kai shekara 15 a sassan duniya, sun karbi cikakkun allurar rigakafin cutar ta HPV.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu
Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75.
An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin.
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A NajeriyaEFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji.
Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala.
Mijinta kuma ya samar da layukan waya da aka yi wa rajista da sunan Fatima Dikko Radda, domin a rikita tunanin mai amfani da manhajar ‘True Caller’.
Bayan matar ta nemi a yi mata canjin dala, sai suka turawa mai canjin lambar asusun banki da zai tura kuɗin kafin ta aika masa da dalar.
Da farko, ta karɓi Naira miliyan 89 daga hannun wani mutum mai suna Aminu Usman, da nufin za ta tura masa dala 53,300.
Daga baya kuma, ta sake karɓar Naira miliyan 108, tana mai cewa za ta tura masa dala 118,000.
EFCC na ci gaba da bincike kan lamarin.