Leadership News Hausa:
2025-03-15@08:50:27 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]

Published: 15th, March 2025 GMT

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]

1. Godiya da harshe:
Wannan yana nufin yabon Allah da faɗar ni’imominsa da kuma ambatonsa a cikin kalmomi. Wannan yana da muhimmanci saboda yana nuni da cewa mutum ya gane cewa Allah ne mai bayar da ni’ima. Hadisin da aka kawo yana nuna cewa mutum idan ya bayyana ni’imomin Allah, to yana cikin masu godiya.

Wannan na iya kasancewa ta hanyar zikirai, du’a’i, da yabonsa da albarkar da yake bayarwa, da cewa Allah Ya yi min ni’ima iri kaza da kaza.

2. Godiya da gaɓɓai:
Wannan yana nufin amfani da dukkan gabban jiki wajen yin biyayya ga Allah da nisantar saɓon Sa. Misali, idan mutum yana da lafiyar jiki, to ya yi amfani da lafiyar wajen aikata kyawawan ayyuka kamar sallah, azumi, sadaƙa, da taimakon jama’a. Idan kuma mutum yana da arziki, ya yi amfani da shi wajen tallafa wa marasa hali da hidimtawa addini. Wannan yana tabbatar da cewa godiya ga Allah ba kawai yana cikin harshe ba, har ma yana cikin aiki.

3. Godiya da zuciya:
Wannan yana da alaƙa da imani da ilimi. Yana nufin mutum ya gane cewa duk wata ni’ima daga Allah take, ba wai saboda ya cancanta a ba shi ba saboda wani abu da ya yi wa Allah, a a sai dai domin Allah yana da rahama da falala da jin ƙai. Wannan yana hana girman kai da alfahari, domin mutum zai fahimci cewa Allah Yana bayar da ni’ima a matsayin kyauta, ba lallai ne saboda ibadarsa ba. Wannan yana ƙarfafa tawali’u da jin haƙuri idan mutum bai samu abin da yake so ba.

A taƙaice, maganar Ibnu Juzai tana koyar da cewa godiya ba kawai fadar “Alhamdulillahi” ba ce kawai, a a, tana da sassa guda uku: da suka haɗa da harshe, da aiki, da kuma zuciya. Idan mutum yana godiya ta waɗannan hanyoyi, to zai zama cikakken mai godiya ga Allah. Wannan yana ƙarfafa imani, yana ƙara ni’ima, kuma yana kusantar da bawa ga Ubangijinsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan Wannan yana

এছাড়াও পড়ুন:

Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi

Jihohin Sakkwato da Kebbi na fuskantar ƙalubale sakamakon cutar sanƙarau da ta ɓulla a jihohin, inda rahotanni suka tabbatar da cewa cutar ta kashe aƙalla mutum 50, yayin da sama da mutum 200 suka kamu da cutar.

A Jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu ne suka fi fuskantar matsalar, inda cutar ta fara yaɗuwa kafin a ɗauki matakan gaggawa.

Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya

A Jihar Sakkwato kuwa, ƙaramar hukumar Tambuwal ce ta fi fama da cutar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka sanar da ɗaukar matakan daƙile cutar domin hana ta yaɗuwa zuwa sauran yankunan.

Dalilin Yawaitar Cutar

Masana kiwon lafiya sun danganta yawaitar cutar da tsananin zafi da ake fama da shi a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ke haifar da bushewar iska da kuma saurin bazuwar ƙwayoyin cutar sanƙarau.

Rashin isassun matakan rigakafi da kuma ƙarancin kula da lafiyar jama’a a wasu yankuna na daga cikin dalilan da suka sa cutar ke bazuwa cikin sauri.

Matakan da Aka Ɗauka

Gwamnatocin jihohin Kebbi da Sakkwato sun ce sun fara ɗaukar matakan gaggawa, inda ake gudanar da allurar rigakafi domin daƙile cutar, musamman ga ƙananan yara da tsofaffi, waɗanda suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Hakazalika, an ƙara wayar da kan jama’a kan alamomin cutar da matakan kariya, domin daƙile yaɗuwarta a cikin al’umma.

Abubuwan da Jama’a Ke Buƙata

Duk da matakan da hukumomi ke ɗauka, har yanzu jama’a na buƙatar ƙarin taimako, musamman wajen samun ingantattun cibiyoyin lafiya da isassun magunguna.

Akwai buƙatar gaggauta aika ƙarin kayayyakin kula da lafiya da ƙarfafa rigakafi domin hana aukuwar cutar a nan gaba.

A halin yanzu, hukumomin lafiya na ci gaba da sa ido kan lamarin, tare da jan hankalin jama’a da su guje wa cunkoso da kuma kai marasa lafiya asibiti da wuri idan suka fara ganin alamomin cutar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi
  • Karancin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Yana Damun ‘Yan Kasa
  • Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
  • Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Filato 
  • Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu
  • Senegal ta yi Allah-wadai da tsare ‘yan kasarta a Mauritania
  • Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM
  • Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi