Amurka Ta Ce Bata Bukatar Jakadan Kasar Afirka Ta Kudu A Kasar, Bayan Da Ya Aibata Shugaba Trump
Published: 15th, March 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka ta ce bata bukatar samuwar jkadan kasar Afrika ta kudu Ebrahim Rasool a kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa Rasool mutum ne wanda yake nuna wariya, yake kuma kin Amurkawa.
Rubio bai bayyana dalilan daukar wannan matakin a kan jakadan ba, amma hakan ya faru ne bayan da Jakadan Rasool ya wata cibiyar bincike na Afrika ta kudu inda a jawabin da ya gabatar ya zargi shugaban kasar Amurka Donal Trump da, da samar da shirin “sake maida Amurka kasa babba” da wani shirin fifita fararem Amurka a kan sauran mutane a duniya.
Labarin ya kara da cewa tun lokacinda Trump ya sake dawowa fadar white house aka hana jakadan Afirka ta kudu a kasar ganawa da jami’an fadar white House kamar yadda ya dace. Fakon haka Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafin da take bawa kasar Afrika ta kudu saboda karar da ta shigar kan HKI wacce ta aiwatar da kissan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 har zuwa yanzun. Banda haka kasar ta sami goyon baya daga kasashen duniya da dama. Kuma gwamnatin Amurka ta bukata Afirka ta kudu ta janye karar amma taki amincewa.
Ya zuwa yanzu dai kotun ta ICC ta fidda sammacin kama Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yauf Galant. Kafin haka dai Ebrahim Rasool ya taba zaman jakadan Afrika ta kudu a kasarAmurka daga shekara ta 2010-2015 a lokacin shugabancin Barak Obama
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yaya ‘Yan Siyasar Amurka Ke Kasafta Harajin Ramuwar Gayya?
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp