Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya.

Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci.

A jiya Jumma\a 14 ga watan Maris na ko wace shekara ne Majalisar ta ware a matsayin ranar yaki da kin addinin musulunci ta duniya.

Iranawani ya bayyana cewa kasashen Turai da daman a da hannu a cikin kokarin raba ayyukan ta’addanci ga addinin musulunci, tare da kafa dokokin wadanda suke bawa wasu damar wulakanta addinai da kona littafansu masu tsarki saboda cusa gaba da kiyyar addinin musulunci da musulmi ga mutanen kasashen su. Da sunan yencin fadin al-barkacin baki.

Daga karshe jakadan ya bukaci kasashen duniya su kakkafa dokoki a kasashensu wadanda zasu bukaci zaman lafiya da mabiya ko wani addini a duniya da kuma kaucewa duk wanda rikicin saboda bambancin addini da kuma nuna wariya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jagora : kiran Trump, na tattaunawa Da Iran yaudarar duniya ne

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya.

 “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba.

“tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?”

“Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar  jama’a na duniya.” Inji jagoran.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a dage takunkumin, yin shawarwari da wannan gwamnatin Amurka, ba za ta cire takunkumin ba. Hakan zai sa takunkumin ya kara tsananta tare da kara matsin lamba,” in ji Jagoran.

Yayin da yake mayar da martani kan zargin da kasashen yammacin duniya ke yi na cewa Tehran na neman makaman nukiliya, Jagoran ya sake jaddada cewa Iran ba ta son kera makaman kare dangi, inda ya kara da cewa da ta yi niyyar yin hakan da ta yi shi ya zuwa yanzu.

“An ce ‘ba za mu bar Iran ta samu makaman nukiliya ba.’ Da muna son kera makaman nukiliya, da Amurka ba za ta hana mu ba.

Gaskiyar ita ce ba mu da makaman nukiliya, saboda mu da kanmu ba ma son su saboda wasu dalilai.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Sin, Rasha Da Iran Sun Yi Kira Da Dakatar Da Matakin Kakaba Takunkumi Na Bangare Guda
  • Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
  • Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta
  • Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare
  • An Bukaci Jama’a Su Rika Binciken Lafiyarsu Don Kare Kai Daga Cutar Koda
  • ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
  • Jagora : kiran Trump, na tattaunawa Da Iran yaudarar duniya ne
  • ECOWAS ta kaddamar da rundunarta mai dakaru 5,000 don yakar ta’addanci
  • Ministan Yaki Na HKI Yace Sojojin HKI Zasu Ci Gaba Da Zama A Kasar Siriya Har’abada