Nageriya ta Maida Martani Kan Zargin Kissin Kiristoce A Kasar,Wanada Gwamnatin Amurka Ta Yi Mata
Published: 15th, March 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya a Abuja ta musanta zargin da cewa ana kishe kiristoci a kasar.
Jaridar Premium timnes ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa rahotannin da suka yada wannan karaiyar sun son ingiza gwamnatin Amurka ta dauki Najeriya a cikin jerin kasashen da suke nuna bambanci a cikin mutanen kasashensu.
A ranar laraban da ta gabata ce kwamiti mai kula da al-amuran Afirka a majalisar dokokin kasar ta bukace gwamnatin Amurka ta dauki mataki a kan Najeriya saboda abinda ya kira kissan kiristoci a Najeriya . Shugaban karamin kwamitin Chris Smith yayi kira ga shugaba Trump ya dorawa Najeriya takunkuman tattalin arziki masu tsanan kan wannan zargi
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai.
An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun.
Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun irin ma’adinan da kasar Ukraine zasu bawa Amurka saboda biyan kudaden da take binta basgi. Har’ila yau Amurkawan sun gabatar da shawarar kasashen biyu su hada giwa don samun riba tare a aikin hakar Ma’adinan.