Zulum ya bai wa jami’an tsaro kyautar gidaje da motoci a Borno
Published: 15th, March 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa jami’an ‘yan sanda kyautar gidaje 280 tare da bayar da gudunmuwar motoci 110 da babura 500 domin inganta tsaro a jihar.
Wannan shiri na da nufin inganta jin daɗin jami’an tsaro da kuma ƙarfafa yaƙi da aikata laifuka da ta’addanci.
MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3A wajen bikin rabon kayayyakin a Maiduguri, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa gwamna Zulum kan goyon bayansa ga jami’an tsaro.
Ya ce wannan tallafi mataki ne mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno.
“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen kula da jin daɗin jami’an da ke sadaukar da rayuwarsu don kare al’umma,” in ji Zulum.
“Waɗannan motoci za su taimaka wajen inganta zirga-zirga da hanzarta kai ɗauki a lokacin buƙata.”
Egbetokun ya bayyana wannan gudunmuwa a matsayin wani babban ci gaba.
“Wannan tallafi zai ƙarfafa gwiwa da inganta ayyukan jami’anmu,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa jagorancinsa wajen tallafa wa jami’an tsaro.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da kayan aiki da duk wani abu da zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Manyan jami’an tsaro, ciki har da shugabannin ’yan sanda da sojoji, sun halarci taron, inda suka jaddada buƙatar haɗin gwiwa don tunkarar ƙalubalen tsaro a jihar.
Ga hotunan a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jami an Tsaro kyauta jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna
Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar.
Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu shida da ke ƙaramar hukumar, inda ya jagoranci ɗaukacin jami’an majalisar ƙaramar hukumar don gudanar da ziyarar.
’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — ObasanjoA dai cikin makon nan ne Shugaban ƙaramar hukumar tare da tawagarsa suka ziyarci fadar Sarkin Kagoma, Mista Paul Zakkah Wyom; Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu; da Tum Nikyob, Mallam Tanko Tete. Ya bayyana godiyarsa tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da aikinta cikin gaskiya da amana.
Ya jero wasu daga cikin nasarorin da majalisarsa ta cimma, ciki har da biyan kuɗin WAEC da JAMB ga ɗalibai 550 da kuma samar da guraben aiki ga wasu ‘yan yankin. Ya kuma jaddada ayyukan ci gaba da Gwamna Uba Sani ke aiwatarwa, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin gwiwa.
A yayin da suke mayar da martani, sarakunan gargajiyan sun yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa ziyarar da ya kawo, tare da gabatar masa da matsalolin da suka addabi yankunansu, ciki har da lalacewar hanyoyi, rashin ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya, ƙarancin ruwan sha da kuma matsalolin tsaro.
Ziyarar ta ci gaba a ranar Laraba zuwa masarautun Zikpak, Godogodo, da kuma Barde, inda a kowanne fada, Mista Dogara ya sake jaddada ƙudirinsa na kyautata rayuwar al’umma da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin majalisar ƙaramar hukumar da sarakunan gargajiya.
Agwam Zikpak, Mista Josiah Kantyok, ya nanata buƙatar zaman lafiya a matsayin tushen ci gaba. Hakazalika, Sarkin Godogodo, Reɓerend Dakta Habila Sa’idu, ya roƙi majalisar da ta magance matsalolin kan iyaka tsakaninta da maƙwabtanta, yayin da Sarkin Barde, Mista Njebi Daniel Lemson, ya bayyana damuwarsa kan matsalar tsaro da ke addabar yankinsa.