Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci
Published: 15th, March 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani ɗan majalisar Amurka, Chris Smith, ya yi cewa ana tauye wa Kiristoci ’yancin addini a Najeriya.
Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba su da alaƙa da addini, domin hare-haren ’yan ta’adda na shafar dukkanin Musulmi da Kiristoci.
Tuggar ya ce hare-haren da ake kai wa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ba sa ware mabiyan wani addini.
Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake yaɗa rahotannin da ba su dace ba, waɗanda ka iya haddasa rarrabuwar kawuna a ƙasar.
Rahoton wata ƙungiya mai suna Open Doors ya ce kashi 89 na Kiristocin da ake kashewa a duniya na faruwa ne a Najeriya.
Sai dai ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta musanta hakan, inda ta ce Musulmi ne ma aka fi kashewa a tashe-tashen hankulan da ake fama da su.
Tun a zamanin mulkin Trump, Amurka ta saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna tauye ’yancin addinin Kiristoci.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matsalar tsaro zargi Gwamnatin Tarayya ta
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara.
NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar NajeriyaHaka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama da waɗanda suka yi karatu mai zurfi.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba matsalar rashin aikin yi da kuma hanyoyin da za a iya bi don magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan