HausaTv:
2025-03-15@16:19:57 GMT

 Rasamani: Asarar Yakin HKI Ta Kai Dalar Amurka Biliyan 14

Published: 15th, March 2025 GMT

Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka.

Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.

Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.”

Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki domin fito da tsarin aiki na sake gina wuraren da yakin ya rusa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi  wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar.

Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako da ke neman Iran da ta shiga tattaunawa kai tsaye tare da Amurka dangane da batun shirinta na nukiliya.

A baya dai Trump da kansa ya yi ikirari a wata hira da Fox Business cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Jami’ai daban-daban na Iran ciki har da Araghchi, sun yi watsi da ikirarin na Trump.

Baya ga haka kuma Iran ta sha nanata cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa da amurka a karkashin matsin lamba ko barazana ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas Tace A Shirye Take Ta Sake Fursinonin HKI Da Amurka, Tare Da Gawaki Wasu Guda 4
  • HKI Tana Cigaba Da Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon
  • Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta
  • Matsalar Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna
  • Shugaba Vladimr Putin Na Kasar Rasha Ya Amince Da Tsagaita Wuta A Yakin Ukraine
  • 2027: Na Shirya Tsaf Don Yin Aiki Tare Da Peter Obi Don Ceto Ƙasar Nan, Gwamnan Bauchi
  • Duniyarmu A Yau: Martani Jagora Ga Trump kan Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Rasha  na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran
  • Nazarin CGTN: Manufofin Haraji Na Amurka Sun Rage Kwarin Gwiwa Kan Kasuwar Hannayen Jari Ta Kasar