HausaTv:
2025-03-15@16:19:57 GMT

 Sojojin Kungiyar  “SADC” Sun Janye Daga DRC

Published: 15th, March 2025 GMT

Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar.

Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro.

Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023.

Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa mayakan M 23 damar kwace iko da Goma da Bukavu.

Ana zargin kasar Rwanda da cewa ita ce ke taimaka wa ‘yan tawayen na M23, tare da aike sojoji 4000 da suke yaki a tare da ita.

A gefe daya, hukumar Agaji ta MDD tana yin kira ga kungiyoyi kasa da kasa da su taimaka su hana bullar babbar matsalar ‘yan gudun hijira da tabarbarewar harkokin agaji a cikin kasar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Na Cigaba Da Ba Da Rarar Kudi Ga Alhazan 2023

 

Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna tana kira ga dukkan alhazan da suka yi aikin hajji ta hannunta a shekarar 2023 da har yanzu ba a biya su rarar kudin da Hukumar Kula da aikin Hajji ta Kasa (NAHCON)ta dawo wa da Alhazan ba, cewa an rubuta masu takardar cek ta banki da za su je banki kai tsaye su karbi kudadensu.

 

 

Saboda haka, hukumar tana sanar da Alhazan da suka fito daga kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da Kajuru, Igabi, Chikun, Birnin Gwari, su hallara a Cibiyar Musabakar Karatun Alkuráni a Kinkinau Tudun Wada Kaduna gobe Alhamis da Jibi Jumaáh 12 da 13 ga Maris don karbar wannan cek na kudadensu tun daga karfe 10 na safe.

 

 

Alhazan kananan hukumomin Ikara, Kubau, Kudan, Makarfi, Giwa, Soba, Sabon Gari da Zariya su hallara a hedkwatar Karamar hukumar Sabon Gari Ranar Asabar 14 ga Maris 2025 don raba masu cek na kudadensu na rara tun daga karfe 10 na safe.

 

 

Sauran alhazai da suka fito daga shiyya ta uku, wato Kudancin Jihar Kaduna, za su hadu a Cibiyar yi wa maniyyata Bita dake Kachiya ranar Lahadi 15 ga Maris don su karbi na su cek din.

 

 

Hukumar tana jawo hankalin alhazan cewa shaidar da take bukatar kowane alhaji ya gabatar it ace lambar kujera da kuma fasfo da suka yi aikin hajji a shekarar 2023.

 

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jumhuriyar Najer Ta Bukaci Tarayyar Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi A Kasar
  • Hamas Tace A Shirye Take Ta Sake Fursinonin HKI Da Amurka, Tare Da Gawaki Wasu Guda 4
  •  An Yi Gargadi Akan Rushewar Kungiyar  Agajin Falasdianwa Ta UNRWA
  • HKI Tana Cigaba Da Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon
  • Sojoji sun ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Filato 
  • Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare
  • Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
  • Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Na Cigaba Da Ba Da Rarar Kudi Ga Alhazan 2023
  • Ministan Yaki Na HKI Yace Sojojin HKI Zasu Ci Gaba Da Zama A Kasar Siriya Har’abada