Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina
Published: 15th, March 2025 GMT
Dakarun Sojin Saman Najeriya (NAF), sun kashe manyan shugabannin ’yan bindiga guda biyu, Gero (Alhaji) da Alhaji Riga, tare da wasu mayaƙansu sama da 20 a wani hari ta sama da suka kai a Jihar Katsina.
Harin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.
Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin KanoRundunar Operation Fansan Yamma ta NAF ce ta ƙaddamar da harin bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar maharan.
A cewar Mataimakin Kakakin NAF, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce dakarun sun lalata sansanin maharan.
“An kashe ƙarin ‘yan ta’adda a tsaunukan da ke kusa, kuma har yanzu ana ci gaba da binciken irin ɓarnar da aka yi musu,” in ji shi.
Gero da Riga sun shahara wajen bai wa ‘yan ta’adda mafaka, waɗanda ke yawan kai matafiya hare-hare a kan titin Funtua zuwa Gusau.
Mutuwarsu ta zama babban ci gaba ga jami’an tsaro da ke aiki tuƙuru don tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
“Wannan babban ci gaba ne a yaƙin da muke yi da ɓarayin daji a Katsina da kewaye.
“Sojojin sama tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa za su ci gaba da kai wa maɓoyar ‘yan ta’adda hare-hare har sai an samu cikakken zaman lafiya,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari Shugabannin Yan Bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Bam Ya Halaka Mutum 8, Ya Jikkata Wasu Da Dama A Borno
Wasu karin majiyoyi sun nuna cewa, wannan hanyar ta hada Maiduguri da wasu kananan hukumomi da ke kudancin jihar Borno, wacce ta kasance yankin da yan ta’addan Boko Haram ke yawan kai hare-hare tsawon shekaru.
A baya hanyar, ta kasance a rufe amma Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum ya bude ta, domin bai wa jama’a damar ci gaba da zirga-zirga a yankin da suka hada da Damboa, Chibok da sauran kananan hukumomi a kudancin Borno tare da taimakon rakiyar sojoji a matsayin kariya.
An kwashe wadanda suka rasun tare da wadanda suka jikkata, wanda har yanzu ba a tantance adadinsu ba, zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar likitoci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp