A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace.

Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala.

A ‘yan kwanakin nan, magoya bayan Manchester United sun ci gaba da nuna fushinsu kan iyalan Glazer, masu mallakar sama da kashi 70 na kulob ɗin.

Har ila yau, Ratcliffe bai samu cikakken goyon baya daga ma’aikatan ƙungiyar ba tun bayan zuwansa a shekarar da ta gabata.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ƙungiya ƙwallo Radcliffe

এছাড়াও পড়ুন:

An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim.

An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma.

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin.

Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a.

Ya buƙaci shugabannin yankin da su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

An tsinci gawar Zainab Ibrahim, wacce aka ɗaura mata aure a baya-bayan nan, kwance cikin jini a gidanta da ke unguwar Warware.

Lamarin ya tayar da hankalin al’umma, lamarin da ya tilasta hukumomi ɗaukar matakan tsaro cikin gaggawa.

Bayan tattaunawa, an amince da sanya dokar hana fita daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na Asuba, tare da kafa wuraren binciken tsaro.

Shugaban kwamitin tsaro na Ƙaramar Hukumar Hadejia, Ahmed Ari, ya bayyana cewa dokar hana fitar za ta taimaka wajen rage aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma roƙi al’ummar yankin su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar waɗannan matakai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa
  • Akwai ’yan ƙwaya a cikin sarakunan gargajiya — Obasanjo
  • Wasu sarakunan gargajiya na ta’ammali da ƙwayoyi — Obasanjo
  • An kama malama tana lalata da ɗalibinta
  • Amurka Ta Ce Bata Bukatar Jakadan Kasar Afirka Ta Kudu A Kasar, Bayan Da Ya Aibata Shugaba Trump
  • Rashford Ya Koma Tawagar Ingila Bayan Shekara Ɗaya
  • Dan Majlisa Ya Tallafa Wa Al’ummar Mazabarsa Da Kayan Abinci Na Naira Miliyan 45 A Katsina
  • An Cire Maguire Cikin Tawagar Ingila Da Za Ta Buga Wasan Neman Gurbi
  • Manchester United Ta Kai Zagayen Gaba Na Gasar Europa League