Kasar Sin Na Adawa Da Zarge-Zargen G7 Don Gane Da Tekun Kudancin Kasar
Published: 15th, March 2025 GMT
Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada.
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar.
A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
MDD ta bukaci masu ruwa da tsaki a Yemen da su kai zuciya nesa
Babban sakantaren MDD António Guterres, ya yi kira ga mabambantan bangarori masu ruwa da tsaki a Yemen da su yi iyakacin kokarin yin hakuri da juna, su kuma dakatar da kowane irin matakin soja, inji kakakinsa a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, “Mun lura da cewa, Amurka ta kai hare-hare da dama kan wasu wurare dake karkashin ikon ‘dakarun’yan Houthi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kowane matakin soja da za a dauka na iya tsananta halin da ake ciki, zai kuma haifar da mummunan tasiri, tare da gurgunta yanayin kwanciyar hankali a Yemen, kana zai kara kamarin kalubalen halin jin kai a kasar.”
‘Yan Houthi dai sun yi barazanar karin kai hare-hare kan jiragen ruwa dake ratsa tekun maliya”.