Aminiya:
2025-03-17@08:39:34 GMT

Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa

Published: 15th, March 2025 GMT

’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya. 

Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata.

’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu

Kudin hatsi irin su shinkafa da wake da masara da dawa da gero da fulawa da kuma cimaka ’yan kamfani da ake sarrafawa daga fulawa kamar taliya da garin samanbita, duk sun yi kasa.

Wasu majiyoyi sun danganta faduwar farashin da janye haraji kan wasu nau’ukan abincin da ake shigo da su daga kasashen waje da Gwamnatin Tarayya ta yi.

An samu kai a wannan yanayi ne a lokacin da manoma suka riga suka sayar da kusan daukacin amfanin gonar da suka noma da damina ga ’yan kasuwa.

Akwai yiwuwar karin sauki — Dan kasuwa

A zantawarsa da Aminiya kan yadda faduwar farashin ta shammace su, wani mai sayar da kayan abinci a Babbar Kasuwar Garin Kubwa da ke Abuja, Alhaji Almustafa Imam, ya ce al’amarin ya dagula masu lissafi, da za su jima ba su warware ba.

Amma ya ce gara hakan, idan aka kwatanta da yadda suka rika fuskantar hauhawar farashi akai-akai sama da shekara guda da ta gabata, a duk lokacin da suka koma kasuwa don saro kaya.

“A lokacin dole sai mun yi cikon kudi don iya sayen adadin abin da muke saya,” in ji shi.

Ya ce saukar farashin kayan abincin na yanzu ya sa abokan huldarsu na sayan karin kaya a wajensu, sabanin yadda a baya suke rage adadin da suka yi niyyar saya saboda tashin farashi.

Dan kasuwan ya ce akwai yiwuwar samu karin sauki idan rage farashin mai da Matatar Dangote ta sanar ya yi tasiri a harkar sufuri, ta yadda za a samu sauki kudin jigilar amfanin gona daga kauyuka zuwa kasuwanni, kuma zai taimaka wa wajen rage kudin da manoman rani ke kashewa kan man fetur a injunansu na ban-ruwa.

Shinkafar waje ta fi ta gida sauki

Da ya ke bayani kan farashin kayan abincin, Alhaji Almustafa Imam ya ce, lamarin har ya kai ga shinkafa da kamfanonin gida ke sarrafawa tana neman fin wadda ake sayowa daga kasar waje saukin farashi.

“Idan zan yi misali da shinkafa da ake kawowa daga kasar Indiya, akwai wadda ake sayarwa a kan Naira dubu 87, a yayin da ta kamfanin gida kwatankwacinta mai nayin kilo 50 mai suna Big Bull ke kai naira dubu 89.” in ji dan kasuwan.

“A bangaren gero kuwa, na sayi buhu mai nauyi kilo 100 a kan naira dubu 72 a lokacin kaka, sai ga shi a yanzu ya karye ya koma naira dubu 62. Wake mafi daraja da ake kira ‘iron beans’ kuwa, na sayi buhu a kan naira dubu 130 a lokacin kaka, amma yanzu ya koma naira dubu dari da goma.

“Wake da ke biye da ‘iron beans’ a daraja a kan naira dubu 95 aka sayar da shi a lokacin kaka, sai ga shi a yanzu ana samun sa a kan naira dubu 80 a wuraren da ake zuwa sari kamar garin Kontagora, da ke jihar Neja, in ji dan kasuwan, wanda ya ce akwai nau’ukan wake da ba su kai wadannan daraja ba da ake samu a kan naira dubu 70.

Ya ce yakan sayi kayan ne a lokacin kaka ya ajiye don gudun bacin rana, amma sai ga shi wannan karon farashin ya karye.

Dan kasuwar ya bukaci gwamnati da ta wadata manoma da kayan aiki a damina mai zuwa don rage farashin abin da ake nomawa a cikin gida, maimakon dogaro da na waje, wanda ya ce ba shi da tabbas.

Kayan kamfani ma sun yi sauki 

Alhaji Muhammadu Dan Saleh da ke gudanar a kasuwanci a Babbar Kasuwar IBB da ke garin Suleja a Jihar Neja ya ce an samu saukin farashin kayan masarufi na kamfani kamar garin samambita da semolina da taliya da makaroni da sauransu.

Ya bayyana cewa kafin watan azumi suna sayar da kwalin taliya Mai Kwabo a kan naira dubu 17, amma yanzu ya karye ya koma kimanin naira dubu 15.

Taliyar Glden Penny kuma, a baya suna sayar da ita a kan naira dubu 21, amma a yanzu ta koma dubu 20.

Buhun sukari na Dangote mai nauyi kilo 50 da a baya ake sayarwa naira dubu 82, a ya koma naira dubu 79 duk da kamawar watan azumi.

Ya ce, wasu kayan na kara farashi ne a lokacin da aka fuskanci yankewarsu a kasuwa, inda ya bayar da misali da cewa “kwalin madarar ruwa ta Peak da a baya an yi lokacin da ta kai naira dubu 45, yanzu tana samuwa a kan naira dubu 43 duk da karuwar bukatarta da ake yi a lokaci irin wannan na watan azumi.”

Ga koshi ga kwanan yunwa

Wasu da Aminiya ta zanta da su sun yaba da saukin farashin kayan abincin da aka samu, sai dai sun yi korafin cewa idan ba a yi dace ba, ’yan kasuwan ne za su sake saye kayan, a nema a rasa a kasuwa.

Wani ma’aikacin gwamnati a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja, Malam Abdullahi Alamuna, ya ce ma’aikata da dama da ya kamata su ci gajiyar saukar farashin, ba a biya su albashinsu na watan Fabrairun da ya gabata ba, sai bayan kamawar sabon wata da kwana hudu.

Hakan, in ji shi, ya sa yawancinsu “ba su iya yin cefanen kayan abinci azumi ba a farkon watan, sannan kasuwanni ba su samu hadahada bayan karban albashi ba, sun kasance cikin karancin ciniki, duk kuwa da saukin kayan abincin da ka samu.”

Shi ma wani mazaunin Abuja, Malam Isa Adamu Rimin Kebe, ya ce “’yan kasuwa da dama a kasuwannin birni na kin sauke farashin kayan abinci duk da saukin da aka samu, inda suke la’akari da farashin tsohon kaya da suka sayo.”

Ya ci gaba da ceaw, “hakan ta sa jama’a da dama da ke neman cin gajiyar saukin da aka samu zuwa kasuwannin kauyuka don samun rangwamen da ya dace.

Hakan ya saba da lokacin da ake samun tashin farashin kayan abinci a kai-akai a baya, inda a wani lokaci waya kadai ’yan kasuwan ke yi da inda suke saro kaya, sai nan take su kara farashi.

Azumin bana sai godiya — Magidanta

Wani magidanci a garin Kaduna, Malam Umar Ramalan Direba, ya ce, “Gaskiya babu abin cewa sai godiya ga Allah, saboda azumin bana dai kam sai godiya ga Allah.

“Ko ba ka da kudin saye za ka ji dadin cewa abinci ya sauka. A bara gero mun saya dubu 1,400 mudu zuwa 1,500 amma sai ga shi a bana kasa da dubu daya.

 “’Yan kasuwa sun wasa wukarsu domin sayar wa jama’a kaya da tsada, amma sai ga shi Allah Ya kamasu, abubuwa suka yi sauki.

“Shi ya sa duk wani magidanci ya samu natsuwa ko da kuwa ba shi da kudin saya domin a bara babu kudi kuma kaya da tsada, ina amfani,” in ji shi.

Abdulmomin Babangida Shehu wani magidanci mai aikin gadi a Kaduna ya ce a yanzu an samu karin masu bayar da taimakon kayan abinci saboda abubuwa sun yi sauki.

“Duk da cewa ba muna son a bamu ba ne kyauta, amma idan abinci ya yi sauki kowa zai samu na ci da budabaki. Shi ya sa muke cikin jin dadi a bana. Domin akwai bayin Allah masu taimako don Allah, ke nan a bana za su samu damar kara taimakawa marasa galihu,” in ji shi.

Shi ma Rimi, wani mai sayar da man fetur a Mogadishi Kaduna cewa ya yi hakika magidanta “Muna cikin farin ciki a bana saboda saukin farashin kayan abinci da aka samu.

“Domin ba a taba samun saukin kayan abinci a lokacin Ramadan ba sai a bana. Sai dai akwai rashin kudi a hannun mutane amma duk da haka muna jin dadin, saukin da aka samu musamman a kasuwanni. Masu shaguna ne kurum suka ki yin sauki,” in ji shi.

Rimi ya kara da cewa a yanzu  masu cirani sun fi son su hada kudi su sayi kayan abinci su girka da kansu a kakunansu a maimakon su saya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kasuwa Ramadan farashin kayan abincin farashin kayan abinci a kan naira dubu kayan abinci a saukin farashi watan azumi

এছাড়াও পড়ুন:

Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3)

12.Yadda a zahiranci abubuwa suke
A shekarar 2006,Carol Dweck wani masanin yadda mutum mai hankali yake,ya san yadda halin mutum yace a cikin littafinsa mai suna “rayuwar mutum da yadda hankalinsa yake” da wasu halayen da aka sa suke a littafinta.” mai suna:The Psychology of Success ko kuma hanyoyin da ake bi ko amfani da su domin a samu dama ta cimma nasara.Kamar dai yadda tunanin Dweck ya ke,mutane wadanda suke da mabambantan halaye suna yi wa kaddarori a matsayin wani hazikanci ne ta bangaren ilim wato kokari wanda akan gane a farkon rayuwa,wanda irin hakan na sa a fuskanci wadansu tarnakai ko matsaloli da za a ga kamar ba za a iya maganinsu ba.Sai dai kuma ta wani hasashen akwai wadansu da suke ganin cewa shi lamarin kokkari ko hazikanci da kirkirar wani abu ana iya samaun damar yin hakan amma idan aka sa hakuri.

13. Ka iya tunkarar duk yadda dalibi yake
Dalibai da z aka koyar a matsayinka na Malamain su suna iya ko maganar gaskiya kowane daga cikin su akwai irin renon daya samu ta harkar ilimi kasancewarsu daga wurare daban daban, nau’oin dabarun da suke da sun a yin abubuwa,ga kuma matsaloli, dole ne kuma ka kwana cikin shirin lalle sai ka sadu da su duk kuwa da irin mizanin da suka cimmawa wwajen koyo.Wannan yana nufin ka tabbatar da kana da badara ko basirar da zaka iya tafiya da koyar da dalibai wadanda dabarar da ko salon da aka yi amfani da su wajen koya masu ya sha bamban dana saura duk a cikin aji daya ko kuma kungiya daya.Nan wani wuri ne inda wadansu abubuwa kamar a iya tafiya da irin halin da aka tsinci kai,ko lamarin tausayi, hakuri, wurin da za su aiki ko amfani ke nan ga su ma’abota ilimi.

14.Samun bambancin yadda aka koyar da daliban da suka bambanta da juna
Idan aka tattara ko tattaro abubuwa mabambanta akan darussa da kuma irin nau’in darussa da kuma sassan ko bangarori hakan yana nunawa dalibai yadda harkoki suke tafiya, da kuma aikin yadda ake maganin matsala yake in ana magana ta babu wasu boye- boye ne, yadda lamarin rayuwar yake a bayyane.
Idan har aka ce shi Malami ko kai Malami duk baka ko baka mallaki dukkan halayen kirki wadanda ake bukatar Malamin makaranta ya kasance yana da su ba,ba damuwar kanka o tada hankalinka zaka yi ba, ka sa a ranka cewar akwai wadansu abubuwan da suka kunshi su halayen inda zaka iya karuwa da su ta hanyar yin gwaji wadda ba mai wata wuya ba ce.Ko dai ta kasance kai babbar manufarka bata wuce ka samu damar ba wadanda basu da lakar fasaha ko wayo ba su kasance su farka daga barcin daya dauke su yayin da su kuma masu kwazon an kara masu kaimi,ko kuma su samu ko a koya masu sabbin dabaru masu kaifi sosai,takardar shedar ilimi ta digiri ko wadda bata kai hakan ba, wata dama ce ta mallakar shi ilimin da kwarewar da kai Malami kake bukata domin ka samu cimma burinka na abinda ka sa gaban sai ka kai can makura ko gaba da ita.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Darajar Kasuwar Kayan Aikin Likitancin Kasar Sin Ta Kai Yuan Triliyan 1.35
  • Yadda za a girka ‘Kamoniya’
  • Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3)
  • Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Gaggauta Dakatar Da Karin Caji A ATM
  • Dan Majlisa Ya Tallafa Wa Al’ummar Mazabarsa Da Kayan Abinci Na Naira Miliyan 45 A Katsina
  • Dangote Da NNPCL Sun Koma Teburin Tattaunawa Kan Cinikin Danyen Mai A Kan Naira
  • Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo
  • Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
  • Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya