Harin da Isra’ila ta kai ya kashe Falasdinawa 9 a arewacin Gaza
Published: 15th, March 2025 GMT
Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya.
An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar.
A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar.
“An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar hula Mahmoud Bassal.
Shaidu da sauran ‘yan jarida sun ce mutanen da ke cikin motar na wata kungiyar agaji ve a garin, kuma Sun samu rakiyar ‘yan jarida da masu daukar hoto lokacin da harin ya same su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina
’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi.
NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafiWani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.
“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.
Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.