Hamas ta yi Allah wadai da haramcin da Amurka da EU suka yi wa gidan talabijin na Al-Aqsa
Published: 15th, March 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci ta Falasdinu da ke da alaka da kungiyar gwagwarmayar.
Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na toshe muryar Falasdinawa.
Sanarwar da Hamas ta fitar ta kara da cewa, wannan shawarar toshe ‘yancin watsa labaru ne da kuma hakki na al’ummar Falasdinu na a ji muryarsu a duniya.
Hamas ta yi kira ga cibiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su yi Allah wadai da wannan shawarar, kuma kada su yi shiru dangane da cin zarafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.
Bisa shawarar hadin gwiwa da Amurka da EU suka cimma, za a ci tarar duk wani sashe na tauraron dan adam da ke yada shirye shiryen tashar talabijin ta Al-Aqsa bisa zargin da ake mata na “yada ayyukan ta’addanci.”
Ita ma a nata bangaren, kungiyar Jihad Islami ta Falastinu ta yi tir da haramcin da aka yi wa tashar talabijin din ta Al-Aqsa, tana mai cewa wani hari ne da nufin murkushe muryar Falasdinu da kuma hana al’ummar kasar isar da sakonin ukubar da suke fuskanta ga duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Ba Jakadan Afirka ta Kudu Sa’o’i 72 Ya fice daga kasar
Amurka ta baiwa jakadan Afrika ta Kudu a kasar wa’adin sa’o’i 72 na ya san idna dare ya yi masa.
Hakan dai na zuwa ne bayan da Amurkar ta ce ba ta maraba da Jakadan na Afirka ta Kudu a kasar Ebrahim Rasool.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya zargi jakadan da na Afrika ta Kudu da nuna “kiyayya” ga shugaban Amurka Donald Trump.
Marco Rubio ya ce Ambasada Ebrahim Rasool “yana kara ruruta wutar rikicin kabilanci kuma gwamnatin Trump ba ta da wani abin da za ta ce masa.”
Tuni Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta mayar da martani inda ta ce ta yi na’am da matakin.
Sanarwar ta ce “abin takaici ne korar jakadan na Afirka ta Kudu a Amurka” inda “ta kuduri aniyar kulla alaka mai amfani da moriyar juna” da Washington.
Rahotannin sun ce jakadan ya bayyana a wata cibiyar nazari ta Afirka ta Kudu inda ya yi ikirarin cewa yunkurin Trump na Make America Great Again, tare da tasirin Elon Musk da mataimakin shugaban kasa JD Vance, wani bangare ne na al’amuran duniya na fifita farar fata.
Dama dai dangantaka tsakanin Amurka da Afrik ata kUdu ta yi tsami sakamakon matsayin Pretoria kan hakkin Falasdinu.
Kasar Afrika ta Kudu dai ta kasance kan gaba a shari’ar da kotun kasa da kasa ta ICJ ke yi na zargin gwamnatin Isra’ila da kisan kiyashi a Gaza.
A watan da ya gabata ne dai fadar White House ta sanar da dakatar da tallafin da Amurka ke baiwa Afirka ta Kudu a matsayin martani ga karar Afirka ta Kudu da ke gaban kotun ICJ.