HausaTv:
2025-03-17@04:07:23 GMT

Amurka Ta Ba Jakadan Afirka ta Kudu Sa’o’i 72 Ya fice daga kasar

Published: 15th, March 2025 GMT

Amurka ta baiwa jakadan Afrika ta Kudu a kasar wa’adin sa’o’i 72 na ya san idna dare ya yi masa.

Hakan dai na zuwa ne bayan da Amurkar ta ce ba ta maraba da Jakadan na Afirka ta Kudu a kasar Ebrahim Rasool.

 Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya zargi jakadan da na Afrika ta Kudu da nuna “kiyayya” ga shugaban Amurka Donald Trump.

Marco Rubio ya ce Ambasada Ebrahim Rasool “yana kara ruruta wutar rikicin kabilanci kuma gwamnatin Trump ba ta da wani abin da za ta ce masa.”

Tuni Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta mayar da martani inda ta ce ta yi na’am da matakin.

Sanarwar ta ce “abin takaici ne korar jakadan na Afirka ta Kudu a Amurka” inda “ta kuduri aniyar kulla alaka mai amfani da moriyar juna” da Washington.

Rahotannin sun ce jakadan ya bayyana a wata cibiyar nazari ta Afirka ta Kudu inda ya yi ikirarin cewa yunkurin Trump na Make America Great Again, tare da tasirin Elon Musk da mataimakin shugaban kasa JD Vance, wani bangare ne na al’amuran duniya na fifita farar fata.

Dama dai dangantaka tsakanin Amurka da Afrik ata kUdu ta yi tsami sakamakon matsayin Pretoria kan hakkin Falasdinu.

Kasar Afrika ta Kudu dai ta kasance kan gaba a shari’ar da kotun kasa da kasa ta ICJ ke yi na zargin gwamnatin Isra’ila da kisan kiyashi a Gaza.

A watan da ya gabata ne dai fadar White House ta sanar da dakatar da tallafin da Amurka ke baiwa Afirka ta Kudu a matsayin martani ga karar Afirka ta Kudu da ke gaban kotun ICJ.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi  wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar.

Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako da ke neman Iran da ta shiga tattaunawa kai tsaye tare da Amurka dangane da batun shirinta na nukiliya.

A baya dai Trump da kansa ya yi ikirari a wata hira da Fox Business cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Jami’ai daban-daban na Iran ciki har da Araghchi, sun yi watsi da ikirarin na Trump.

Baya ga haka kuma Iran ta sha nanata cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa da amurka a karkashin matsin lamba ko barazana ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Afirka Ta Kudu Ta Caccaki Amurka Kan Korar Jakadanta Daga Washington
  • Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka
  •  Iraki: An Kashe Shugaban Kungiyar “Da’esh” Na Iraki Abdullahi Makki
  • Amurka Ta Ce Bata Bukatar Jakadan Kasar Afirka Ta Kudu A Kasar, Bayan Da Ya Aibata Shugaba Trump
  • Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin Amurka
  • MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP
  • Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
  • ‘An Kwashe Shekaru Ana Kashe Kudaden Yaran da ba a ma Haife su ba a Nijeriya’
  • Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta