Sakamakon Neman ’Yancin Taiwan Zai Kai Yankin Ga Halaka
Published: 15th, March 2025 GMT
A baya-bayan nan, jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te, wanda ya kira kansa da “mai rajin neman ‘yancin kan Taiwan”, ya kara ikirarin cewa bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ba sa karkashin ikon juna, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokradiyya ce mai mulkin kanta. Amma duk yunkurin Lai Ching-te ba zai iya canza gaskiyar da duniya ta amince da ita ba, wato Taiwan ba ta taba zama kasa ba, kuma ba za ta taba zama ba a nan gaba.
Ta yaya za a warware batun Taiwan? Tuni dai babban yankin kasar Sin ya tabbatar da cewa, a shirye yake ya yi iyakacin kokari da sahihiyar zuciya domin neman kyakkyawar makomar dinkewar kasar Sin cikin lumana. Amma idan ‘yan aware masu neman “’yancin Taiwan” suka yi tsokana ko tilasta neman ballewa ko ma tabo batu mai tada kura, dole ne zai dauki matakai masu tsauri. Lai Ching-de da mabiyansa da ke wasa da wuta a mashigin tekun Taiwan, za su kone kansu. Sin za ta hada yankunanta, kuma tabbas za su dunkule. Wannan shi ne yanayin tarihi da ba za a iya juyawa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp