Tsohon Firaministan Lebanon: Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba
Published: 16th, March 2025 GMT
Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa.
A cikin ‘yan shekarun nan, an samu rashin fahimta, shakku har ma da suka game da ci gaban da kasar Sin ta samu cikin lumana, da tasirinta a duniya. Dangane da haka, Diab ya ce, duk wadannan ba za su hana kasar Sin samun ci gaba a fagen duniya ba. Ya ce, wadanda ba sa son ganin yadda kasar Sin ke kara cimma nasara, suna bukatar karfafa hulda da jama’ar kasar don kara fahimtar kasar. Kuma ya zama dole su amince da gaskiyar cewa kasar Sin ta bunkasa har ta zamanto babbar kasa a duniya a matakai da yawa, kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a yayin tabbatar da bunkasuwar kasashe daban daban a duniya. Ya kara da cewa, kamata ya yi su yarda tare da fahimtar hakan cikin natsuwa tare da gina wata gadar tuntubar juna da Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutane 7 Sun Mutu, Kadarorin Miliyan 50.3 Sun Salwanta Dalilin Gobara A Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci.
Sanarwar da Kabiru Isah Jaafar ya fitar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ta bayyana cewa kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 50.3 sun lalace sakamakon gobara, yayin da aka ceto wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 180.3. Haka kuma, an ceto rayuwa mutane bakwai da daga gobarar.
Sabon Kwamishinan ‘Yansanda Ya Kama Aiki A Kano ‘Yansanda Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Dogo Saleh, A AbujaHukumar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sani Anas ta shawarci al’umma da su kula da amfani da wuta domin guje wa afkuwar gobara. Haka nan, an yi kira ga direbobi da su bi dokokin hanya, musamman a manyan tituna, don rage afkuwar haɗura da kare rayuka da dukiyoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp