Masarautar Hadejia Ta Raba Zakka Ta Kimanin Naira Miliyan 63 Ga Mabukata
Published: 16th, March 2025 GMT
Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa.
Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa.
Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da zakkarsu ga kwamitin masarauta don rabawa mabukata.
Tun da farko, Hakimin Birniwa, Sarkin Arewan Hadejia, Alhaji Abubakar Usman Kariya, ya jinjinawa kwamitin zakka na gundumar bisa zakka da aka tara a gundumar.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
MDD : Kwamitin Sulhu ya yi tir da kisan kiyashin Siriya
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya a kasar, da su kare “dukkan ‘yan Syria ba tare da nuna bambanci ba,” ba tare da la’akari da kabila, addini ba.
Majalisar ta yi kakkausar suka kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a lardunan Latakia da Tartus tun daga ranar 6 ga Maris, ciki har da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula, musamman a cikin al’ummar Alawite, ‘yan tsirarun da ke da alaka da dangin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad.