Aminiya:
2025-03-16@09:04:05 GMT

Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi

Published: 16th, March 2025 GMT

A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a daurin auren.

Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman amarya da kuma Rainahatu Sulaiman (’yar uwar amarya) da Misbahu Ahmad (abokin ango) da direban motar sun tafi garin Murno da ke da nisan kilomita 5 daga Boto domin gaisawa da ’yan uwan amaryar kamar yadda aka saba a al’adar Hausawa.

Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar

A kan hanyarsu ta zuwa garin ne suka yi hatsarin da ya yi sanadiyar mutuwar angon da ’yar uwar amaryar yayin da ita kuma amaryar da sauran mutane uku da ke cikin motar, suka tsallake rijiya da baya da munanan raunuka.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wani mahaukaci ne ya yi sanadiyyar hatsarin a yayin da yake ƙoƙarin tsallaka titi.

An ce direban ya yi iya ƙoƙarinsa don kauce wa mahaukacin, amma motar ta ƙwace masa ta yi sama, sannan ta faɗo ƙasa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata sauran uku da ke cikinta.

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, angon ya samu mummunan bugu a kansa, nan take ya mutu, ’yar uwar amaryar kuma ta rasu ne a asibiti a yayin da ake yi mata magani.

Ita kuma amaryar ta samu karaya a ƙafarta da kuma rauni a hannunta da kafadarta, yayin da direba da abokin angon suka samu raunuka a hannu da ƙafafu.

Mahalarta ɗaurin aure sun shiga alhini

Daruruwan mahalarta ɗaurin auren daga nesa da kusa da suka yi dandazo a garin Boto domin bikin sun faɗa cikin dimuwa da jimami bayan faruwar lamarin, mintoci 30 kafin daurin auren.

Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne a ƙarshen makon shekaranjiya da misalin ƙarfe 1:35 na rana.

Wani ɗan uwan angon mai suna Alhaji Saminu Abubakar Boto, ya bayyana yanayin da al’umma ke ciki a matsayin abin baƙin ciki matuƙa.

Ya ce, “Asara ce da ba za a iya misalta ba. Al’umma gaba ɗaya suna alhinin rasuwar sirikina da kuma kanwata Raihanatu.

“Iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su sun fada cikin ruɗani, inda ’yan uwa da abokai ke kokawa kan kan wannan babban rashi, ba zato ba tsammani.”

Alhaji Boto ya bayyana cewa gidan dangin amaryar da ke cikin hidimar ɗaurin auren, ya koma wurin zaman makoki da zubar hawaye bayan afkuwar lamarin.

An garzaya da mahaifin ango asibiti

Bayan samun labarin faruwar lamarin, nan take mahaifin angon ya yanke jiki ya faɗi aka garzaya da shi asibiti, inda likita ya bayyana cewa jininsa ya hau 260 sama da 220.

Ita ma mahaifiyar angon ta faɗi lokacin da aka ba ta labarin rasuwar ɗanta.

Alhaji Boto ya ce, “Har zuwa lokacin da nake magana da ke, ’yar uwata, amaryar ta kasance cikin kaduwa da tashin hankali.

“Ban san yadda zan kwatanta lamarin ba. Lallai abin tausayi ne. Sama da mutane 4,00 ne suka shiga gidanmu domin jajantawa bisa wannan bala’in da ya faru,” inji shi.

Ya bayyana Marigayi Musa a matsayin “Saurayi mutumin kirki mai mutunci da kamun kai wanda ya yi fatan kafa iyalinsa tare da ‘yar uwata, Maryam Suleiman, amma da yake Allah Ya sa hakan ba zai yiwu ba saboda rasuwarsa.

Ganawar ƙarshe

“Angon na zaune ne a garin Buruku da ke Jihar Filato. Ya zo Boto daga Jos ne domin ɗaurin aurensa, sai muka yi ta barkwanci tare da abokai, ‘yan mintoci kadan kafin su wuce kauyen Murno.

“Cikin zolaya yake ce min in je in sa babbar-riga. Na ce masa idan na saka, mutane za su dauka ni ne ango. Muka yi dariya. Da gama hirarmu suka tafi Murno domin gaishe da ”yan uwa. Sai dai kash, maganata ta ƙarshe da shi ke nan.

“Lokacin da za a je ɗaura auren ni ne na ɗauko babana da abokansa a motata zuwa gidan amaryar, bayan mun isa aka aiko ana nema na a babban asibitin kusa da gidan amaryar. Da na je aka shaida min cewa motar da ta kai ango ƙauyen Murno ta yi hatsari.

“Da isowata na tarar da gawarsa a shimfide a kan gadon da yankan karfe ko gilashi a kansa, a yayin da amaryar, Maryam, Raihanatu, Misbahu da direban motar ke karɓar magani wurin masu ba da agajin gaggawa. Bayan mintoci kaɗan kuma aka tabbatar da mutuwar Raihanatu.

Yankan ƙauna

“Za a riƙa tunawa da Raihanatu a matsayin ‘yar uwa wacce ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara bikin auren da ba a cika yin irinsa ba.

“Ta shiga mota ita da ango zuwa Murno domin ita da amarya ne kawai suka san gidan danginmu na ƙauye; kuma a al’adance, amarya ba za ta bude fuskarta don jagorantar direba ba.

“Wannan mummunan lamari ya jefa al’umma cikin ruɗani, inda yawancin mazauna garin suke bayyana shi a matsayin daya daga cikin ranaku mafi bakin ciki a cikin ‘yan kwanakin nan.

“Ba mu taɓa ganin irin wannan abin takaici irin haka ba a cikin wannan gari. Za a daɗe iyalai da abin ya shafa ba su manta wannan lamarin ba,” in ji shi.

Wakilin Aminiya ya ta tattaro bayanan cewa an yi jana’izar duk mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada jim kaɗan bayan faruwar hatsarin, yayin da amaryar ke cikin mawuyacin hali sakamakon mummunan raunuka da kuma rashin masoyi da ‘yar uwarta a ranar da ya kama ta tafi kowace farin ciki a wajenta

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Amarya Hatsari Jihar Bauchi Jihar Filato Mutuwa ɗaurin auren

এছাড়াও পড়ুন:

Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar.

Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne.

A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani otel da ke birnin Baledweyne da wata mota da aka shakare da bama-bamai, kafin daga bisa suka shiga cikin otal din suka kai farmakin da ya dauki tsawon yini guda.

Majiyoyin ‘yan sandan sun tabbatarwa kamfanin dillanmcin labaran Reuters cewa, hudu daga cikin ‘yan ta’addan sun tarwatsa kansu, yayin da kuma jami’an tsaro suka halaka biyu daga cikinsu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Al-Shabaab kungiyar da ke da alaka da Alqaida, ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce mayakanta sun kashe mutane 20 da suka hada da sojoji da shugabannin kabilu.

Shugabannin kabilu daga yankin Hiran sun hallara a otal din domin tattaunawa kan yadda za a tunkari ayyukan ta’addancin kungiyar Al-Shabaab da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa  a tsakanin al’ummar kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka – SSANU
  • Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
  • Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
  • Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna
  • Peter Obi ya yi ganawar sirri da gwamnan Bauchi
  • 2027: Na Shirya Tsaf Don Yin Aiki Tare Da Peter Obi Don Ceto Ƙasar Nan, Gwamnan Bauchi
  • Peter Obi Ya Ziyarci Bauchi, Ya Gana da Gwamna Bala Mohammed
  • Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi