HausaTv:
2025-03-16@09:53:16 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 102

Published: 16th, March 2025 GMT

102-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suak zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na m,aulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda Khalifanci Khalifa na biyu ya kasance. Inda kamar yadda wasu sahabban manzon All..(s) suka yi korafi ga khalifa na farko, kafin ya yi wafati, haka ta kasance, wato Khalifa na biyu, ya kasance mai tsanani ga mutanensa, yana duka, yana tsawatawa, kuma ya tsare wasu sahabban manzon All..(s), ya hanasu fita madina saboda kada su yada hadisan da baya son su yadu.

Basu sami sauki ba sai bayan mutuwarsa.

Sannan munji cewa shi ne ya fara fifita sahabban manzon All..(s) a rabon dukiya, inda ya fifita matan m,anzon All..(s) kan kowa, sannan wadanda suka je yakin Badar, sannan muhajirun sannan ansara da sauransu.

Daga karshe wannan ya samar da wasu sahabbai masu dukiya sosai da kuma wasu talakawa sosai don rabonsu kadan ne. mun ji cewa imam Ali (a) ka kauracewa majalisunsa, sai da wasu dalilai, don kada su ji tsaron yana kokarin kwace iko daga gareshi, wannan hakan zai sa kafirai su debe kauna wajen kauda daular musulunci tana jaririya. .

Sannan mun bayyana cewa a lokacin Khalifancinsa ne aka kada daular Farisa da kuma Roma. Daular musulunci ta sami dukiya mai yawa, sannan mun bayyana cewa, sau da dama Khalifa Umar yana komawa ga Amirulmuminina (a) don neman fatawa kan al-amuran addini.

Sannan yakan bada shawara wani lokaci a karba wani lokaci kuma, musamman idan al-amarin ya shafi siyasa ba zai karbaba. Sannan munji yadda Abu lulu’a ya kashe shi, saboda takura masa wanda mai gidansa mughira yake yi, sannan da ya kai kararsa wajen Khalifa, khalifa ya goyi bayansa.

Bawan Mughira ya kasance ba farishe ne, ya shiga masallaci ya sokeshi da wuka har sau ukku daya daha cikinsu a karkashin cibinsa, wanda kuma shi ne ya kashe shi.

Sannan mun ji cewa dansa Abdullahi dan Umar, bayan da ya tabbata babansa ba zai rayuwa bay a bashi shawara ya nada Khalifa, sai yace, idan ya nada, Abubakar ya nada, idan bai nada ba manzon All..(s) bai nada ba.

A lokacinda Umar ya debe kauna daga rayuwar, sai ya fara tunanin abokansa wadanda suka taimakawa Abubakar wajen kwace khalifanci daga hannun Amirul Muminin (a). sai yana cewa, da Ubu ubaida dan Jarrah yana nan da na nada shi khalifa, don shi amintaccen wannan al-ummar ne, da salim maula Abukhzaifa yana nan da zan nashi shi…don shi mai tsananin son All..T ne.  

Duk sun mutu, ba wanda ya rage daga cikin wadancan abokan aiki. Ya manta da Amirulmuminina (s), wanda shi ne kofar ilmin manzon All..(s), shi ne mijin diyarsa Fatimah(s), shi ne yake da sabika a musulunci, wanda ba wanda yake da shi a cikin dukkan sahabban manzon All..(s) yana da rai amma Khalifa Umar ya manta da shi.

Daga karshe ya yanke shawarar kafa shura ta mutane shida inda ya umurcesu su zabi daya daga cikinsu a matsayin Khalifa a bayansa a cikin kwanaki uku, sannan ya sanya Aliyu dan Abitalib(a) da ya daga cikinsu, amma ya san ba yadda za’a yi su zabi Ali(a) a matsayin Khalifa. Kai yayi da yadda Uthman dan Affan zai zama Khalifa.

Sheik Kashifin Ghida, ya bayyana shoora na mutum shida a matsayin wani makirci ga Amirul muminina (a), na tilastawa al-umma khalifancin Khalfa Uthman, wanda kuma daga karshe an ga sharrin da khalifancin nasa ya jawowa musulmi da kuma addinin musulunci.

Kafin yam utu Umar ya kira mutanen guda shiga a lokaci guda, sai yace masu (shin kowa daga cikinku yana kwadayin khalifanci a bayana)? Ba wanda ya bashi amsa. Sai ya sake tambaya, sai Zubai ya bashi amsa yana cewa: Me zai nesantamu da ita, kaima ka rike ta, ka kuma tafiyar da ita,  ba kuma abinda ka fimu da shi a cikin kuraishawa, ko kuma a abinda ka gabatarm ko kuma a kusanci ga manzon All..(s).

Sai ya juya a garesu, ya ce masu, shin ba zan fada maku, kan kawukanku ba, sai suka ce : Da mun nemi afwa a gareka da ba zaka amince mana ba.

Sai yafara bayyana ra’ayinsa dangane da su, sai yace: Kai ya Zubair, mumunin a lokacinda ka yarda da abu, a lokacinda kayi fushi kuma kafiri na, wata rana mutum wata rana kuma shaidani ne…All..ba zai taikamaka ka hada kan wannan al-umma ba.

Sai ya cewa Talha, in fada ko kada in fada. Sai Talha ya ce “…hakika manzon All..(s) ya yi wafati yana fushi da kai saboda wata Magana da kayi a lokacinda ayar hijabi ta sauka)…..

Sai ya kuma wajen Sa’addu dan Abiwakkas, yace shi ma’abucin yaki ne, amma bai cancanci khalifanci ba, don bai iya shugabanci ba.

Sai ya koma wajen, sannan yajuya wajen Abdurrahman dan Auf, yace , amma kai dan Auf, da za’a goda rabin imanin wannan al-umma da naka, da naka zai rinjaya, amma kana da Rauni. Wanda ya sa baka cancanci khalifanci ba.

Sai ya juya wajen Amirul muminina (a) sai yace masa, Amma kai kam, ba don wasanka ba, daidan an doramaka ita da zaka kaisu ga hanya madai daiceya, da zaka kaisu ga hanyar gaskiya.

To amma shi ma ya aibata shi(s) yana shim ai yawan wasa ne. amma duk da haka ya cancani Khalifanci, kuma ya san hanya madaidaiciya. Kuma zai kaisu ga gaskiya.

Sai ya juya wajen Uthman, y ace masa, kai kuma , gata nan, kamar ina gidan khuraishawa sun dora makai ta sannan ka dorawa musulmi danginka Banu Umayya, da kuma banu Ma’eed. Sannan ka bawa danginta dukiyar al-umma, wanda ya sa wasu daga cikin al-umma suka yi maka tawaye, suka kuma yankaka a cikin gidanka.

Idan haka ya faru ka tuna da zance na…}.

Sannan bayan ya san cewa Uthman zai dora bani umaida da kuma banu Mu’eed a kan al-ummar musulmi, sannan zasu yi tawaye, har su kashe shi, me yasa zai Sanya shi dan takarar khalifanci.

Kuma abinda ya faru, kenan, don daga lokacin, wato tun lokacinda aka kashe Uthman al-ummar musulmi ta rabu kashi biyu har yau fiye da shekaru dubu da 1400 suna kafirta juna suka kashe juna.

Sannan , bayan y agama maganarsa, sai ya juya wajen mutane, ya ce, masu manzon All..(s) ya rasu yay ana mai yarda da wadannan mutane 6.  Sannan sai ya fadawa mutanen 6 kan cewa, su kawo wani daga cikin shuwagabannin Ansar, don su basu da wani rabo a shugabancin al-umma, sannan ya ce, : Ku kawo Alhassan dan Aliyu da kuma Abdullahi dan Abbas don suna da kusanci da manzon All.., ina fatan halattansu zai kawo al-barka ga zaman naku. Sai dai basa dawani rabu a cikin al-amarinku. Wato basu da kuri’a a zaben Khalifa.

Sannan ya juya zuwa Abi Talha al-ansari yace masa, : Ya Baban Talha! Lalle All…ya daukaka musulunci da ku, ka zabi mazaje 5 daga cikin Ansar, ku luzumci wadannan mutane, don su aiwatar da umurnina kamar yadda yake, su kuma gaggauta yin haka.

Sannan ya juya zuwa ga Mikdad dau ausad, yan fada masa kamar yadda ya fadawa Abu Talha.

Sannan ya ce masu. Idan mutane 5 sun gamu a kan wani, daya ya ki, ku buge wuyarsa. Idan hudu sun gamu a kan wani, sannan biyu suka ki ku katse wuyan biyu.

Sannan idan uku sun hadu a kan wani, sannan wasu ukkun suka yarda da wani mutum, ku kasance tare da wadanda Abdurrahman dan Auf yake tare da su. Sannan ku kashe sauran idan sun ki amincewa da abinda mutane suka hadu a kansa.

Sai Imam Ali (a) ya tabbatar da cewa, ba zasu zabe shi ba, ya fita daga wajensa yana bakin ciki, sai ya hadu da amminsa Abbas dan Abdulmuttalib, ( r) sai ya ce masa ya ammi an hanamu ita.

Sai Abbas yace masa: Way a fada maka, hakan? Sai yace: Hakika yad ai dai tani da Uthman, sannan yace ku kasance tare da mafi yawa, sannan yace ku kasance tare da Abdurrahaman dan Auf.

Sa’adu dan Abi wakkas ba zai sabawa, dan amminsa, Abdurrahman dan Auf ba, sannan Abdurrahman surukin Uthmanu ne, ba zasu sabawa juna ba, don haka, ko abdurraman ya nada Uthman, ko kuma Uthman ya nada Abdurrahman.

Da haka Amirul muminina (a) a gano makircin da aka yi masa, a wannan shoran tun ba’a zauna ba.

Da wannan dalilin ne Amirul muminina (a) ya kasnace yana bakin ciki da wannan makircin da aka yi masa, hatta bayan da mutane suka zabe shi bayan da aka kashe Khalifa na ukku Uthman dan Affan.

Inda yake fada a khudubarsa ta shakshakiyya: Sai lokacinda zai mutu, ya sanyata a cikin jama’an ya riya cewa ni daya ne daga cikinsu, Ina neman tsari daga All..daga kuma wannan shoora, yauce ne idan an kwatantani da na farkonsu, ake shakkan fifiko na a kansa. Ballanta na wadannan da aka daidaitani da su don zaben khalifa.

Wato akwai a cikin wadannan mutum 5 wadanda suka cancanci khalifanci, ? banda ni.

Masu  sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasance tare da wadanda suka sai ya juya Sai ya juya

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Tace: Amurka Bata Da Hakkin Tsara Mana Yadda Zamu Tafiyar Da Kasar Mu

Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X.

Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi.

Ministan ya kara da cewa, ya maida martani da cewa: Amurka ce da alhakin marawa ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a duniya, kuma gwamnatin shugaban Biden kadai ta kashe dalar Amurka biliyon 23 don kissan Falasdinawa kimani 60000 a Gaza. Don haka yana kira ga Amurka ta dakatar da tallafin da take bawa HKI wacce mafi yawan kasashen duniya ta dauketa a matsayin yar ta’adda.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Tace: Amurka Bata Da Hakkin Tsara Mana Yadda Zamu Tafiyar Da Kasar Mu
  • Salami: Makiyan Iran Ba Su San Wani Abu Ba Sai Karfi
  • ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]
  • MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP
  • Karancin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Yana Damun ‘Yan Kasa
  • Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu
  • Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10
  • Shugaba Vladimr Putin Na Kasar Rasha Ya Amince Da Tsagaita Wuta A Yakin Ukraine