HausaTv:
2025-04-14@16:29:46 GMT

Salami: Makiyan Iran Ba Su San Wani Abu Ba Sai Karfi

Published: 16th, March 2025 GMT

Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo  janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci.

Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara.

Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata barazana.

Bugu da kari kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; Makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran masu kekashewar zukata ne, ba su aiki da mandiki, kuma ba su aiki da duk wata halayya ta ‘yan ta ‘yan adamtaka,abu daya tilo da su ka yi imani da shi, shi ne amfani da karfi.

Har ila yau, kwamandan dakarun kare juyin musuluncin na Iran ya yi ishara da halayyar HKI da Amurka a yakin Gaza, Lebanon, Syria, Yemen, Iraki da Afghanistan; yana mai kara da cewa; sun tabbatar da cewa, su masu karya alkawali ne, don haka batun tattaunawa da  wadannan makiyan  kuskure ne

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kara da cewa

এছাড়াও পড়ুন:

MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara

Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara.

Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki.

Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya ci rayukan mutane da dama da su ka hada mata da kananan yara.

A nata gefen, kungiyar agaji ta “Red- Cross” ta yi gargadin cewa, kayan aikin da ake da su a cikin asibitocin da ake da su a cikin yankin sun kusa karewa.

Haka nan kuma kungiyar ta ce; ” A cikin yankuna da dama na Gaza, ba a iya samun ruwan sha, babu abinci, kuma babu wutar lantarki.

Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza, ta yi kiran gaggawa domin a shigar da kayan aiki a cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya. Haka nan kuma ta kara da cewa, da akwai masu fama da ciwon suga 80,000 sai masu hawan jini 110,000 ba su samun kula yadda ya dace.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran
  • Iran Zata Yaye Labulen Ire-Iren Makamanta Na Musamman Da Ta Mallaka Domin Kare Kai
  • Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
  • Dagewa Iran Takunkuman Zalunci Na Daga Cikin Manufofin Tattaunawa Da Amurka: Aref
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
  • Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Amurka da Iran
  •  A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
  •  Limamin Tehran: Iran Ba Ta Tsoron Tattaunawa
  • MDD: Mafi Yawancin Wadanda Yaki Ya Ci A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara
  • An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi