Fiye Da Mutane 20 Ne Su Ka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
Published: 16th, March 2025 GMT
Da safiyar yau Lahadi, sojojin Amurka da Birtaniya sun ci gaba da kai wa kasar Yemen hare-hare, inda a bayan nan su kai wasu jerin hare-hare guda uku.
Yankunan da hare-haren na Amurka da Birtaniya su ka shafa a cikin Yemen sun hada “ali Sabba”, dake gundumar Sahhar, da hakan ya yi sanadiyyar kashe daruruwan dabbobi.
Haka nan kuma sojojin na Amurka sun kai wasu hare-haren a gabashin Majzar, dake gundunar “Ma’arib”.
Tun da marecen Asabar ne dai sojojin na Amurka su ka shelanta kai wa Yemen hare-hare a biranen San’aa,Sa’adah, da Zammar.
A birnin Sa’adah, kananan yara 4 sun yi shahada sai kuma wata mace, yayin da wasu mutane fiye da 10 su ka jikkata.
Wasu yankunan da hare-haren na Amurka su ka shafa sun hada da yankunan Mikra da kuraishiyya a gundumar Baidha’a.
A yankin Jarf, dake birnin San’aa mutane 9 ne su ka yi shahada.
Tashar talabijin din ‘almasirah’ ta kasar Yemen ta bayar da labarin dake cewa jumillar wadanda su ka yi shahada sun kai 24, 14 daga cikinsu a birnin Sanaa,sai kuma 10 a Sa’adah. Haka nan wani adadin da ya kai 23 sun jikkata.
Kungiyar Ansarullah ta Yemen ta jaddada ci gaba da kai wa jiragen ruwan HKI hare-hare a ruwan “Red sea” har zuwa lokacind a za a kawo karshen hana shigar da kayan agaji ga mutanen Gaza masu azumin Ramadan.
Daga marecen jiya Asabar zuwa tsakar dare, sau 30 Amurka da Birntaniyan su ka kai wa Yemen hare-hare.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasashen Turai na E3 sun goyi bayan tattaunawar Iran da Amurka
Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka.
Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya.
A cikin sakon da ya wallafa, Falconer ya yaba da tattaunawar da akayi a babban birnin kasar Oman na Muscat a matsayin “muhimmiyar mataki na farko.”
Kuma a cewarsa “Birtaniya, tare da kawayenta na E3, a shirye suke don tallafawa tattaunawar.
A cikin 2018 a lokacin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma a baya kan shirin nukiliyar Iran da kuma lafta mata tsauraren takunkumai amma kuma ya nuna aniyar kulla sabuwar yarjejeniya don maye gurbin waccen ta 2015.