Kofar JMI A Bude Take Don Tattaunawa Da Kasashen Turai
Published: 16th, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar.
Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi.
A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da Bozorg wadanda iran take takaddama da UAE dangane da mallakarsu, ya ce abu ne wadanda kasashen biyu suke iya warwarewa a tsakaninsu. Banda haka yace dokokin kasa da kasa ma suna iya warware wannan sabanin da ke tsakaninsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Za Ta Kara Yawan Alkamar Da Take Kai Wa Kasashen Afirka
Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7.
Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru.
Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000.
Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400.
Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka. A shekarar 2024 da ta gabata ta kai wa nahiyar alkama da kudinta su ka kai dala biliyan 7.