Aminiya:
2025-03-17@21:35:33 GMT

Yadda za a girka ‘Kamoniya’

Published: 16th, March 2025 GMT

Barkan mu da sake haɗuwa a zauren girke-girke na watan Ramadana. Tare da fatan ana cikin koshin lafiya.

A yau na kawo wa uwargida wani girkin shuwa daga Jihar Borno, wato ‘Kamoniya’ domin yin buda baki. A sha ruwa lafiya.

Abubuwan da za ki bukata:

· Hanta · Tumbi · Huhu · Albasa 3 · Lemun tsami · Attaruhu · Man gyada · Curry da thyme · Maggi da gishiri

Yadda ake hadin:

A wanke kayan ciki (banda hanji), sai a yanka su kanana.

A zuba man gyada a cikin tukunya, sai a dora a kan wuta.

Sannan sai a yanka albasa a zuba man gyadan kadan a cikin tukunyar.

Bayan haka, sai a zuba curry da thyme da gishiri kadan a wankakken kayan cikin. Sai a gauraya su kafin a zuba a tukunya.

Idan an gama gaurayawa, sai a zuba su a tukunya ana juya su har sai ruwan da man sun shiga cikin kayan cikin.

Za a ga kayan cikin sun koma ruwan kasa. Sai a juye a kula a rufe. Hakan za a rika yi kadan-kadan har sai kayan cikin sun kare.

A wanke attaruhu da lemon tsami. A kirba attarugu ya kirbu sosai, sannan sai a zuba maggi wanda zai kashe zafin attaruhun.

Sai a matsa lemon tsami a kan attaruhun.

Ana cin kamoniya ne da wannan hadin attarugun. Ana dangwalawa a attaruhu don samin dandano mai gamsarwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kamoniya kayan cikin

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA sun cafke wasu mutane da hodar iblis da suka ɓoye a cikin carbi da kuma takalma.

A cewar hukumar, an cafke ababen zargin ne yayin da suke ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasa mai tsarki.

Femi Babafemi, darektan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa tare da hotunan hodar iblis ɗin da aka kama.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tattalin Arzikin Al’Ummar Kasar Sin Na Tafiya Yadda Ya Kamata A Watan Jarairu Da Fabrairu
  • Shugaban Kasar Amurka Ya Kara Yawan Kasashen Da Ya Sa Wa Takunkumin Shiga Amurka
  • Darajar Kasuwar Kayan Aikin Likitancin Kasar Sin Ta Kai Yuan Triliyan 1.35
  • HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma
  • Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3)
  • Iran Tace: Amurka Bata Da Hakkin Tsara Mana Yadda Zamu Tafiyar Da Kasar Mu
  • Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi
  • Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa
  • Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka – SSANU