Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya.
Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya.
Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibintaHaka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta.
Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza.
A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a Ƙaramar Hukumar Gwoza.
Rasuwar Hajiya Asta Shehu Timta dai wani babban rashi ne ga masarautar ta Gwoza bisa ga irin gudummawar da ta ke bayarwa ga al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno Sarkin Gwoza Hajiya Asta Shehu Timta
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar.
Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako da ke neman Iran da ta shiga tattaunawa kai tsaye tare da Amurka dangane da batun shirinta na nukiliya.
A baya dai Trump da kansa ya yi ikirari a wata hira da Fox Business cewa ya aike da wasika zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Jami’ai daban-daban na Iran ciki har da Araghchi, sun yi watsi da ikirarin na Trump.
Baya ga haka kuma Iran ta sha nanata cewa ba za ta shiga duk wata tattaunawa da amurka a karkashin matsin lamba ko barazana ba.