Trump ya rushe kafar watsa labarai ta VOA
Published: 16th, March 2025 GMT
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.
Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna.
Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani.
Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya.
Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin Amurka kan me hakan ke nufi, sannan babu wanda zai iya fahimtar ko an rufe kafofin baki ɗaya ke nan.
Shugaban ƙungiyar ’yan jarida a Amurka, William McCarren ya ce wannan ba abin alheri ba ne ga duniya da kuma aikin jarida baki ɗaya, musamman a wannan zamani da ake yaƙi da labaran bogi.
Tuni dai Shugaba Trump ya naɗa ’yar jarida Kari Lake a matsayin daraktar hukumar da za ta kula da rushe waɗannan hukumomi, waɗanda ya zarga da yaɗa labaran nuna masa ƙiyayya.
Sama da shekaru 80 ke nan da kafa VOA wadda ke yaɗa shirye-shiyenta cikin harsuna 40, ta rediyo da talabijin da intanet da shafukan zumunta na zamani.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar.
Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar.
Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci?
NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true