Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma don neman daukaka ya kara da cewa.

A ci gaba da hirar Sadik ya amsa tambayar da aka yi mashi a kan fina-finan da yayi da kuma wadanda yake kallo a matsayin wanda yafi so a cikinsu, inda ya ce daga cikin fina-finan da ya fito wadanda kuma yafi so, akwai Mati Da Lado sai kuma wani fim mai suna Dan Marayan Zaki.

Abinda ya sa nafi son wadannan fina finai shi ne ba don komai ba sai don kawai su na daya daga cikin ayyukan da nafi wahala kuma na kara samun gogewa a wannan sana’a tawa, hakazalika su ne fina-finan da aka fara sanina dasu kuma aka fara sanin wanene Sadik Sani Sadik da kuma abinda zan iya yi idan aka dora mani kyamara.

Daga karshe Sadik ya bayyana sirrin samun daukakarshi a masana’antar Kannywood, da cewa ba komai bane ya sa ya samu daukaka illa addu’ar iyaye da kuma jajircewa saboda na dauki harkar fim a matsayin babbar sana’ar da na dogara da ita yanzu, kuma nike rufawa kaina asiri.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara.

NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya

Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama da waɗanda suka yi karatu mai zurfi.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba matsalar rashin aikin yi da kuma hanyoyin da za a iya bi don magance ta.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
  • Hasashen Samun Ruwan Sama A 2025: Shawarwarin Da Kwararru Suka Bai Wa Manoma
  • Jami’ar Gwamnatin Tarayya Kachia Ta Shirya Tsaf Domin Fara Aiki
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]
  • Sin Ba Za Ta Taba Amincewa Da Ayyukan ’Yan Aware Ba 
  • Wata Rana Za A Yi Wa Gwamnatin Tinubu Sambarka – Minista 
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya
  • Kasar Sin Ce Ke Kan Gaba A Matsayin Kasar Da Ta Fi Samun Jari Daga Ketare