Aminiya:
2025-04-14@17:44:38 GMT

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina

Published: 16th, March 2025 GMT

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga 31 tare da lalata sansaninsu a Jihar Katsina, yayin wasu hare-hare guda biyu da suka kai.

A farmaki na farko, dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da ’yan bindiga a garin Maigora da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.

Abba ya mayar da filin Idi cibiyar harkokin addinin Musulunci Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka

Da farko, sojojin sun kashe ’yan bindiga biyar bayan sun kai farmaki garin.

Sai dai lokacin da suka sake haɗuwa don kai harin ramuwar gayya, sojojin sun sake kashe guda bakwai, ciki har da Dogo, wanda babban Kwamanda ne a cikinsu.

Haka kuma, sojojin sun ƙwace babura guda bakwai da ‘yan bindigar ke amfani da su.

A wani farmakin, rundunar sojojin sama ta yi luguden wuta a maboyar ’yan bindiga da ke dajin Unguwar Goga, Ruwan Godiya, a Ƙaramar Hukumar Faskari.

Sun lalata sansanin shugabannin ’yan bindiga biyu; Alhaji Gero da Alhaji Riga, inda suka kashe aƙalla mahara 19.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin Najeriya na ƙara ƙaimi wajen murƙushe ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, tare da lalata sansaninsu.

Har ila yau, sojojin na ci gaba da sintiri ta sama da ƙasa don daƙile yunƙurin ’yan bindiga na sake hare-hare.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga dakaru hare hare yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar.

Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin yaki na Amurka ne a lokacinda yake tattara bayanai a wasu yankuna a sararin samaniyar kasar.

Masana sun bayyana cewa farashin ko wane jirgi yakin samfurin MQ-9 ya kai dalar Amurka miliyon $33, don haka ya zuwa yanzu kasar Amurka ta yi asarar dalar Amurka miliyon $600.  Kafin haka dai sojojin Yemen bangaren makamai masu linzami sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin Balistic  guda biyu kan HKI, wanda ya kai ga rufe tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv.) . Bugediya Yahyah Saree kakakin sojojin kasar ta Yemen ya bayyana cewa godiya ta tabbata ga All..saboda dukkan makaman sun cimma manufofin cillasu, wadanda suka hada da rufe tashar jiragen sama na Bengrion da tilastawa miliyoyin yahudawan sahyoniyya gudu zuwa wuraren buya.

Saree ya kammala da cewa, ayyukan soje a kan HKI da kuma Amurka zasu ci gaba har zuwa dakatar da yaki a Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
  • Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume
  • Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19
  • An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
  • ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara
  • Janar Tsiga, Mahaifiyar Rarara da muhimman mutane da aka sace a Katsina
  • Gaza: Sojojin HKI Sun Sake Kai Wa Asibitin “Ma’amadani Hari
  • Isra’ila ta yi barazanar fadada hare-hare Gaza yayin da ta yanke Rafah daga birnin Khan Yunis
  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • Yemen Ta Maida Martani Kan Wasu Cibiyoyin Ajiyar Makamai A Yaffa Don Tallafawa Gaza