HausaTv:
2025-03-16@21:52:44 GMT

Hizbullah ta yi Allah wadai da harin Amurka da Birtaniya a kan Yemen

Published: 16th, March 2025 GMT

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama a daren jiya Asabar.

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai kan wasu unguwanni a Sanaa babban birnin kasar, da kuma wasu larduna da dama, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Bayanin ya kara da cewa, “Wannan zaluncin ya zo ne a matsayin wani yunkuri na murkushe wannan al’umma mai girma mai tsayin daka wajen ci gaba da nuna goyon bayanta ga al’ummar Gaza da kuma ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu.”

Sanarwar ta yi nuni da cewa, hare-haren da ake kaiwa fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a kasar Yaman, ya sake bayyana hakikanin gaskiya da mummunar fuskar gwamnatin Amurka, wadda ke aiwatar da ayyukan cin zarafi ga kasashen da ke adawa da manufofinta a yankin da ma duniya baki daya.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana harin da Amurka ta kai birnin San’a a matsayin laifin yaki da kuma keta dokokin kasa da kasa, wanda kuma ya yi dai-dai da irin hare-haren Isra’ila a kan Gaza, Siriya, kuma Lebanon.

 Hizbullah ta ci gaba da cewa: Al’ummar kasar Yemen masu tsayin daka, wadanda suka rubuta kasidu na jarumtaka tare da jinin shahidansu na goyon bayan al’ummar Palastinu da Gaza, kuma suka tsaya tsayin daka a karkashin jajircewar  shugabanninsu, irin wannan al’umma ba za su ja da baya ba wajen tinkarar wannan zalunci na makiya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina 

Dakarun Sojin Saman Najeriya (NAF), sun kashe manyan shugabannin ’yan bindiga guda biyu, Gero (Alhaji) da Alhaji Riga, tare da wasu mayaƙansu sama da 20 a wani hari ta sama da suka kai a Jihar Katsina.

Harin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Faskari.

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci  Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano

Rundunar Operation Fansan Yamma ta NAF ce ta ƙaddamar da harin bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar maharan.

A cewar Mataimakin Kakakin NAF, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce dakarun sun lalata sansanin maharan.

“An kashe ƙarin ‘yan ta’adda a tsaunukan da ke kusa, kuma har yanzu ana ci gaba da binciken irin ɓarnar da aka yi musu,” in ji shi.

Gero da Riga sun shahara wajen bai wa ‘yan ta’adda mafaka, waɗanda ke yawan kai matafiya hare-hare a kan titin Funtua zuwa Gusau.

Mutuwarsu ta zama babban ci gaba ga jami’an tsaro da ke aiki tuƙuru don tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

“Wannan babban ci gaba ne a yaƙin da muke yi da ɓarayin daji a Katsina da kewaye.

“Sojojin sama tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa za su ci gaba da kai wa maɓoyar ‘yan ta’adda hare-hare har sai an samu cikakken zaman lafiya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Da Mutanen Kasar Somalia Sun Ki Amincewa Da Karban Mutanen Gaza
  • Fiye Da Mutane 20 Ne Su Ka Yi Shahada Sanadiyyar Hare-haren  Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
  • Kungiyoyin Falasdinawa Suna  Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
  • Hamas ta yi Allah wadai da haramcin da Amurka da EU suka yi wa gidan talabijin na Al-Aqsa
  • Harin da Isra’ila ta kai ya kashe Falasdinawa 9 a arewacin Gaza
  • Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina 
  • Dan Majlisa Ya Tallafa Wa Al’ummar Mazabarsa Da Kayan Abinci Na Naira Miliyan 45 A Katsina
  • Senegal ta yi Allah-wadai da tsare ‘yan kasarta a Mauritania
  • Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10