Trump Ya Dakatar Da Kafar Watsa Labarai Ta VOA
Published: 16th, March 2025 GMT
Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40.
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.
Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna.
Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke karkashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba.
Haka kuma tuni Trump din ya soma daukar wasu matakai wadanda suka hada da soke kwantiragin da VOA din ke da shi na amfani da labaran kafafen watsa labarai masu zaman kansu daga ciki har da kamfanin dillancin labarai na Amurka wato AP.
Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani.
Sannan kudaden da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke karkashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki daya.
Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin Amurka kan me hakan ke nufi, sannan babu wanda zai iya fahimtar ko an rufe kafofin baki daya ke nan.
Tuni dai Shugaba Trump ya nada ’yar jarida Kari Lake a matsayin daraktar hukumar da za ta kula da rushe wadannan hukumomi, wadanda ya zarga da yada labaran nuna masa kiyayya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum Ɗaya A Bauchi, Wasu Sun Jikkata
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp