Afirka Ta Kudu Ta Caccaki Amurka Kan Korar Jakadanta Daga Washington
Published: 16th, March 2025 GMT
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar.
Hakan na kunshe cikin wata ’yar takaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “dan siyasar wariyar launin fata mai kyamar Amurka,” lamarin da ya kara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria.
A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon zarginta da ƙwace gonakin fararen fata na ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa shugaba Trump ya sanar da cewa duk wani manomi da aka kwace wa gona, kuma yake fatan koma wa Amurka to zai samu izinin zama ɗan ƙasar cikin sauƙi.
Matakin da Amurka ta dauka na korar jakadan Afirka ta Kudu “abin takaici ne,” kamar yadda ofishin shugaban ƙasar Cyrill Ramaphosa ya bayyana a ranar Asabar, yana mai kira ga “gyara diflomasiyya” tsakanin kasashen biyu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40.
Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp