IRGC: Iran ba za ta fara yaki ba amma za ta mayar da martani ga duk wata barazana
Published: 16th, March 2025 GMT
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya.
Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama.
Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”
Shugaban kasar Amurka ya sake alakanta ayyukan da kungiyar Ansarullah ta Yaman ga Iran, ya kuma ce dole ne Iran ta daina goyon bayan kungiyar mai gwagwarmaya.”
Salami ya jaddada cewa, mutanen Yemen al’umma ce mai ‘yanci da ke bin manufofi na kashin kansu ba tare da an yi musu katsalandan ba. In ji babban kwamandan na IRGC.
Salami ya jaddada cewa, “Mu ba al’ummar da ke gudanar da ayyukanta cikin sirri ba ne; a maimakon haka, muna yin komai a bisa doka da oda da kuma kiyaye ka’idoji na duniya, kuma komai namua fili yake, kuma lokacin da muka dauki matakin soji a kan Isra’ila ba mu boye ma kowa ba kamar yadda duniya ta sheda hakan a cewar janar Salami.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu.
Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza.
Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can.
An kuma samu irin wannan halayyar ta yin kira a kawo karshen yakin a tsakanin likitocin soja su 100 sai kuma malaman jami’a su ma daruruwa.
Kiraye-kirayen da sojojii suke yi a HKI da na kwo karshen yakin Gaza da mayar da fursunonin yaki, ya bude wata sabuwar takaddama a tsakanin ‘yan siyasa.
Wasikar ta bude jayayya a tsakanin ‘yan sahayoniya akan cewa, Netanyahu yana ci gaba da yin yaki ne saboda maslahar kashin kansa.